Daga: Sani Idris Maiwaya
Karamar Hukumar Dala ta kaddamar da aikin hanya da za’a Kashe Sama da naira miliyan 197 a yankin Gobirawa Daiba dake Karamar Hukumar.
Da yake kaddamar da aikin shugaban Karamar Hukumar Alhaji Surajo Ibrahim Imam ya bukaci dan kwangilar da zaiyi aikin da yayi aiki mai inganci da nagarta sannan ya sanya matasan yankin a cikin wadanda zasuyi aikin a wasu bangarorin aikin.
Alhaji Surajo Imam ya kuma ce kamfanin Nomora Integrated Service ne aka bawa kwangilar aikin kuma an riga an biyasu kaso hamsin cikin dari na kudin aikin.
Suma wasu mazauna yankin Alhaji Mustapha Abdulmajid A.Z da Naziru Gambo sun bayyana farin cikin su bisa samun wannan aikin suna masu cewar aikin hanyar ya dade yana ci musu tuwo a kwarya.
A karshe cikin wata sanarwa da Jami’ar Hulda da jama’a ta Karamar Hukumar Dala Hassana Aminu ta sanyawa hannu tace wakilin kamfanin da zaiyi aikin Alhaji Tasiu yayi alkawari zasuyi aikin mai inganci da nagarta kuma zasuyi shi akan lokaci.