Daga: Mukhtar Yahaya Shehu
Gwamnatin jihar Kano ta kammala fitar da Iyaka Tsakanin Jami’ar Bayero da yankin Rimin Zakara da ke karamar hukumar Ungogo bayan kawo karshen Takaddamar da ke tsakanin bangarorin biyu.
Kwamishinan kasa da tsare -tsare na jihar Kano Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar ne ya bayyana haka yayin da ya jagoranci kaddamar da aikin fitar da iyakar a garin na Rimin Zakara a Karamar hukumar Ungogo.
Ya ce a wannan lokaci dukkanin Takaddamar da ke tsakanin bangarorin biyu ya kawo karshe kasancewar an fitar da Iyaka Tsakanin Jami’ar Bayero da Kuma sabon birnin da gwamnatin jihar Kano ta fitar wa da Al’umar yankin na Rimin Zakara.

“Daga yanzu duk wanda aka samu da laifin yanka filaye a wurin da aka ware wa Jami’ar Bayero, to ya tabbata Doka za ta yi aiki a Kan sa kasancewar duk masu korafi daga cikin Al’umar yankin suma gwamnatin jihar Kano ta sallame su ta hanyar biyan su Diyyar kudi da Kuma filaye a sabon birnin da aka fitar.” In ji kwamishina Abduljabbar.
Kwamishina Abduljabbar Muhammad Umar ya kara da cewa da zarar an kammala fitar da iyakar gwamnatin jihar Kano za ta bai wa kowanne bangaren takardar shaida da za ta Kare duk wata barazanar cin Iyaka daga Bata-garin Dillalai.
Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar ya ja hankalin Al’uma Kan su kaucewa yin mu’amala bata-garin Dillalai wadanda su ne Suka haddasa wannan tashin tashina. Inda ya ce gwamnatin jihar Kano za ta Sanya kafar wando guda da duk irin wadancan Bata -garin Dillalai idan ta Kama su.

A jawabinsa wakilin Jami’ar Bayero a wurin farfesa Ahmad Muhammad Tsauni ya bayyana farin cikin su bisa wannan rana, inda ya ce Jami’ar Bayero ta fi kowa farin cikin kawo karshen wannan Takaddamar da ta dauki shekaru tsakanin su da Al’umar yankin na Rimin Zakara.
Shi kuwa Shugaban kwamitin Al’umar yankin da ya shiga tsakani domin samun Daidaito Alhaji Baba Habu yaba wa gwamnatin jihar Kano ya yi bisa cika alkawarin kawo karshen wannan Takaddamar da ta gagari gwamnatoci da yawa a baya.
“Ina tabbatar muku cewa tun lokacin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dora wa kwamishinan kasa da tsare -tsare na jihar Kano Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar nauyin cewa ya yi duk abin da ya dace domin kawo karshen Takaddamar. Babu wani lokacin da muka bukaci zama da kwamishinan ya ki amincewa duk kuwa da abubuwan da Suka faru na rashin Dadi daga mutanen yankin saboda fuwata da Suka yi a baya.” In ji Alhaji Baba Habu