Daga: Shehu Suleiman Sharfadi

Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da wani shirin horaswa na musamman ga manyan jami’anta, domin inganta jagoranci, dakile cin hanci da rashawa, tare da farfado da darajar kima da da’a a cikin aikin gwamnati.

Shirin wanda ya gudana a Kaduna, daga ranar Jumma’a zuwa Lahadi, ya hada da mahalarta kamar su kwamishinoni, masu ba da shawara na musamman, daraktoci janar, da sakatarorin dindindin daga sassa daban-daban na gwamnati.

Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen bude shirin, ya bayyana cewa horon wata hanya ce ta gina tubalin gaskiya da amana a cikin shugabanci. Ya ce cin hanci da rashawa ba kawai laifi ne na tattalin arziki ba, har ma da hadari ga ci gaban al’umma da tarbiyyar jama’a.

A cewarsa: “Wannan horo wata dama ce ta gyara tunani da aiki, domin dorewar nagartaccen shugabanci da ingantaccen isar da ayyuka ga al’umma. Gwamnati ba za ta lamunci cin hanci da rashawa ba a kowane mataki.”

Ya kara da cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da daukar matakai na gina hukumomi masu karfi da tsari, wadanda za su tabbatar da adalci da gaskiya a tsakanin ma’aikata da jama’a.

Shugaban Ma’aikatan Gwamnati, Alhaji Abdullahi Musa, wanda ya wakilci Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya ce wannan shiri yana daga cikin manufofin gwamnatin jihar na samar da nagartaccen shugabanci da yaki da cin hanci da rashawa, wadanda suka dade suna hana ci gaba a Najeriya.

Ya jaddada cewa, gwamnati na kallon horar da jami’anta a matsayin zuba jari ne na dogon lokaci, wanda zai taimaka wajen dorewar shugabanci mai inganci a jihar Kano.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Gwamna Abba Ya Yabawa Ganduje Bayan Musuluntar Da Mutane 370 A Kano

Daga: Mas’ud Mato Garo  Gwamnan jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf, ya…

Gwamnatin Kano Ta Fitar Da Iyaka Tsakanin BUK Da Garin Rimin Zakara – Kwamishina Abduljabbar 

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu  Gwamnatin jihar Kano ta kammala fitar da Iyaka Tsakanin…

Sarkin Kano Ya Yaba Wa Ƙoƙarin Tsofaffin Daliban Kano Capital

Daga: Saminu Ibrahim Magashi Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya…

Kungiyoyin Matuka Motocin Kurkura Da Na Manyan Motoci Sun Yi Alwashin Tallafawa Tsaftace Muhalli

Daga: Ibrahim sani Gama Kungiyar matuka motocin korkura ta jihar Kano da…