Daga: Muhammad Adamu Abubakar

Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da kudirin kafa Hukumar kula da ababen more rayuwa ta jihar inda ya zama doka.

Shugaban majalisar Alhaji Jibrin Ismail Falgore ya bayyana hakan a Kano.

Ya ce, an amince da kudirin dokar ne a ya yin zaman sirri.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Alhaji Lawan Hussaini Chediyar ‘Yangurasa ya shaidawa manema labarai cewa, tanadin dokar ya yi hani da fasa hanya domin janyo ruwa ko dasa na’urar sadarwa.

Lawan Hussaini Chediyar ‘Yangurasa ya kuma bayyana cewa, duk wanda aka samu da karya dokar zai biya tara.

Haka zalika, majalisar ta yiwa dokar Hukumar kula da Bunkasa ayyukan noma a yankunan karkara da Hukumar kula da gine-gine da kuma na Hukumar kula da yada labarai ya tsallake karatu na biyu. Wanda ya ba da damar yin mataimaki ga shugaba a hukumomin.

Wakilinmu a Majalisar ya bamu labarin cewa, majalisar ta karbi wata takarda daga Gwamna Abba Kabir Yusuf inda ya ke neman amincewarta domin nada Akitek Ibrahim Yakubu Adamu a matsayin kwamishina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Gwamnatin Jihar Lagos ta Fara yin Gwajin lafiya ga Maniyyata aikin hajjin bana na Shekara 2026

Gwamnatin Jihar Lagos ta Fara yin Gwajin lafiya ga Maniyyata aikin hajjin…

Kano Ta Fara Shirin Dakile Ambaliya, Za Ta Share Dukkan Mugudanan Ruwa — Hukuma

Daga: Ibrahim Sani Gama Hukumar kula da kwashe shara ta jihar Kano ta…

pin up brendinin Azərbaycan istifadəçiləri üçün tətbiq imkanları

pin up Azərbaycanda yükləmə və istifadə bələdçisi pin up brendinin Azərbaycan istifadəçiləri…

Gwamnatin Mu Na Alfahari Da Gidauniyar Dangote

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi    Mataimakin gwamnan jihar Kano kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo…