Daga: Muhammad Adamu Abubakar
Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da kudirin kafa Hukumar kula da ababen more rayuwa ta jihar inda ya zama doka.
Shugaban majalisar Alhaji Jibrin Ismail Falgore ya bayyana hakan a Kano.
Ya ce, an amince da kudirin dokar ne a ya yin zaman sirri.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Alhaji Lawan Hussaini Chediyar ‘Yangurasa ya shaidawa manema labarai cewa, tanadin dokar ya yi hani da fasa hanya domin janyo ruwa ko dasa na’urar sadarwa.
Lawan Hussaini Chediyar ‘Yangurasa ya kuma bayyana cewa, duk wanda aka samu da karya dokar zai biya tara.
Haka zalika, majalisar ta yiwa dokar Hukumar kula da Bunkasa ayyukan noma a yankunan karkara da Hukumar kula da gine-gine da kuma na Hukumar kula da yada labarai ya tsallake karatu na biyu. Wanda ya ba da damar yin mataimaki ga shugaba a hukumomin.
Wakilinmu a Majalisar ya bamu labarin cewa, majalisar ta karbi wata takarda daga Gwamna Abba Kabir Yusuf inda ya ke neman amincewarta domin nada Akitek Ibrahim Yakubu Adamu a matsayin kwamishina.