Daga: Shehu Suleiman Sharfadi

Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada kudirinta na farfaɗo da al’adun gargajiya da kuma bunkasa su, domin tabbatar da cewa matasa na kan gaba ba su manta da tushensu ba.

Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin shirya bikin Kalankuwa Festival (KANFEST 2025), ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a ofishinsa a jiya Juma’a.

A cewarsa, wannan gagarumin biki zai gudana ne daga ranar Asabar 25 ga Oktoba, zuwa Litinin 27 ga Oktoba, 2025. Ya ce an shirya bikin ne domin ba da dama ga musayar ilimi tsakanin tsofaffi da matasa wajen yada harshe, al’adu da dabi’un da suka gina asalin mutanen Kano tun fil’azal.

Kwamared Gwarzo ya bayyana cewa KANFEST 2025 zai zama wata babbar kafa da za ta bai wa ’yan fasaha, masu sana’o’i da matasa masu ƙirƙira damar nuna basirarsu ga duniya, wanda hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan yi da kuma ƙarfafa tattalin arzikin jihar.

Ya kara da cewa, farfaɗo da al’adun Kano na daga cikin muhimman manufofin Gwamna Abba Kabir Yusuf, domin a cewarsa, “Al’ada ita ce ruhin kowace al’umma – ita ce ke bayyana yadda muke rayuwa, tana ɗauke da imani da ƙa’idojin da ke haɗa mu wuri guda.”

Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da irin waɗannan bukukuwa akai-akai domin tabbatar da cewa al’adun gargajiya sun ci gaba da wanzuwa a zukatan matasa da sauran al’umma baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Jaridar BusinessDay ta karrama Gwamnan Jihar Kano da lambar yabon Business Governor of the Year.

Daga Mas’ud Mato Garo Mataimakin gwamnan kano Murtala Sule Garo ne ya…

JATA Ta Karyata Jita-Jitar Tsadar Kayayyakin Noma, Ta Ce Ana Sayar Da Su Cikin Rangwame — DG

Daga: Kabir Getso Hukumar Bunƙasa Harkokin Noma Da Samar Da Abinci Na…

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kaddamar da Rabon Transformers 500 Ga Kananan Hukumomi 44 a Kano

Daga: Sani Idris Maiwaya KANO – Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir…

Kwamandan Hukumar Civil Defense Ta Taya Gwamnatin Kano Alhinin Rasuwar ‘Yan Wasanninta

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Biyo bayan rasuwar ‘yan wasan Kano 22 da suka…