Daga: Shehu Suleiman Sharfadi

Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada kudirinta na farfaɗo da al’adun gargajiya da kuma bunkasa su, domin tabbatar da cewa matasa na kan gaba ba su manta da tushensu ba.

Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin shirya bikin Kalankuwa Festival (KANFEST 2025), ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a ofishinsa a jiya Juma’a.

A cewarsa, wannan gagarumin biki zai gudana ne daga ranar Asabar 25 ga Oktoba, zuwa Litinin 27 ga Oktoba, 2025. Ya ce an shirya bikin ne domin ba da dama ga musayar ilimi tsakanin tsofaffi da matasa wajen yada harshe, al’adu da dabi’un da suka gina asalin mutanen Kano tun fil’azal.

Kwamared Gwarzo ya bayyana cewa KANFEST 2025 zai zama wata babbar kafa da za ta bai wa ’yan fasaha, masu sana’o’i da matasa masu ƙirƙira damar nuna basirarsu ga duniya, wanda hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan yi da kuma ƙarfafa tattalin arzikin jihar.

Ya kara da cewa, farfaɗo da al’adun Kano na daga cikin muhimman manufofin Gwamna Abba Kabir Yusuf, domin a cewarsa, “Al’ada ita ce ruhin kowace al’umma – ita ce ke bayyana yadda muke rayuwa, tana ɗauke da imani da ƙa’idojin da ke haɗa mu wuri guda.”

Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da irin waɗannan bukukuwa akai-akai domin tabbatar da cewa al’adun gargajiya sun ci gaba da wanzuwa a zukatan matasa da sauran al’umma baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Kungiyar ‘Yan Jarida Ta Kasa Reshen Gidan Rediyon Tarayya Pyramid Za Ta Kulla Alaka Da Kamfanoni Domin Cigaba

Daga: Muhammad Adamu Abubakar  Shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen Gidan Rediyon…

An bayyana shugabar hukumar taimakekeniyar lafiya ta jihar Kano kachima Dr. Rahila Aliyu Mukhtar amatsyin Mace wadda baza amance da ita ba a harkokin lafiya a jihar Kano.

An bayyana shugabar hukumar taimakekeniyar lafiya ta jihar Kano kachima Dr. Rahila…

Jami’ar Al-hikma Ta Bada Gurbin Karatun Mutum Uku Kyauta Daga Iyalan Mamatan ‘Yan Wasan Kano

  Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Biyo bayan rasuwar ‘yan wasan Kano 22…

Mataimakin Gwamnan Kano Ya Kai Ziyarar Farko K/H Gwarzo Bayan Rantsar Da Shi

Daga: Shehu Suleiman sharfadi  Jim kadan bayan rantsar da Sabon Mataimakin Gwamnan…