Daga: Shehu Suleiman sharfadi 

Jim kadan bayan rantsar da Sabon Mataimakin Gwamnan jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo ya kai ziyara karamar hukumar Gwarzo domin shaida karbar katin jam’iyyar APC na Sanata Bello Hayatu Gwarzo.

Mataimakin Gwamnan wanda ke tare da manyan ‘yan siyasa, ya samu kyakkyawar tarba daga dandazon al’umma da suka fito kan Titi domin taya shi murna tare da yi masa fatan alkhairi a sabon mukamin nasa

Akan hanyar sa daga kano zuwa gwarzo ya kwashi saoi da dama kafin ya karasa garin gwarzo sakamakon daruruwan mutane da suka fito kan hanya domin tarbarsa.

Wakilinmu na Ofishin Mataimakin Gwamna ya rawaito cewa, akwai fitattun yan siyasa a garin Gwarzo ciki har da tsohon mataimakin gwamnan jihar kano injiniya Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo da sanata Bello Hayatu da tsohon kwamishina Alhaji Ibrahim Dan Azumi da sauran wasu da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Gwamnatin Kano Ta Aike Da Tawaga Sokoto Don Ta’aziyyar Rasuwar Sardaunan Sokoto

Daga: Mas’ud Mato Garo Wani ayari na manyan jami’an Gwamnatin Jihar Kano ya…

Dawowar Abba Kabir Yusuf APC Zai Haifar Da ‘Da Mai Ido A Kano – Tumfafi

Daga: Ibrahim Sani Gama Sakataren Kungiyar Kasuwar Abinci ta Duniya da ke…

Mataimakin Gwamnan Kano Ya Bayyana Wasanni a Matsayin Hanya ta Hadin Kai da Bunkasa Tattalin Arziki

Daga: Shehu Suleiman sharfadi  Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo,…

Kungiyar Jami’an Tsaro Na Sa Kai Tana Taka Rawar Gani Ba Tare Da An Sanyasu A Tsarin Biyan Albashi Na Kasa

Daga: Ibrahim Sani Gama Kungiyar Jami’an Tsaro na Sa Kai ta Kasa reshen…