Daga:  Abdullahi Bashir 

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta shawarci matasan Najeriya da su rungumi ɗabi’ar haƙuri da godiya, tare da gujewa rayuwar roƙo da gaggawar neman cimma nasara ba tare da aiki tuƙuru ba.

Ta bayyana hakan ne a yau Juma’a yayin da ta karɓi shugabannin reshen matasa na jam’iyyar APC a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. A wajen taron, ta kuma bai wa shugabannin matasan motocin bas guda tara domin tallafa musu wajen gudanar da ayyukansu.

A cewar sanarwar da Babbar Mai Taimaka mata kan Harkokin Yaɗa Labarai, Busola Kukoyi, ta fitar, Uwargidan Shugaban Ƙasar ta buƙaci matasa su rungumi aiki tuƙuru, haƙuri, gaskiya da riƙon amana a matsayin ginshiƙan samun nasara.

Ta ce Allah ne kaɗai Ya fi sanin abin da kowanne mutum yake buƙata, tana mai cewa yawancin matasa na son komai cikin gaggawa.

Ta ƙara da cewa, tana ƙoƙarin koya musu muhimmancin gamsuwa da abin da suke da shi maimakon rayuwar roƙo da dogaro da wasu.

Oluremi Tinubu ta kuma yi amfani da misalin tsuntsun Mikiya, inda ta ce idan ya ga hadari ba ya tsorata, sai dai ya yi amfani da damar wajen shawagi sama da shi. Ta ce hakan ya kamata ya zama darasi ga matasa, su kasance masu juriya tare da neman hanyarsu ta samun nasara ba tare da kwaɗayin abin da wasu suke da shi ba.

Har ila yau, ta yaba wa shugabannin matasan APC saboda haɗin kai da suke nunawa wajen ƙarfafa jam’iyyar tun daga matakin ƙasa har zuwa ƙananan hukumomi. Ta kuma buƙace su da su ci gaba da bayyana nasarorin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma manufofin Ajandar Sabunta Fata Nagari ga al’umma.

Domin ƙarfafa ayyukan reshen matasan jam’iyyar, Uwargidan Shugaban Ƙasar ta miƙa motocin bas guda tara ga Shugaban Matasan APC na Ƙasa, mataimakinsa, shugabannin shiyyoyi da kuma shugabannin reshen Abuja domin amfani da su wajen ayyukan jam’iyya da hidimar al’umma.

Da yake jawabi a madadin waɗanda suka amfana, Shugaban Matasan APC na Ƙasa, Dayo Israel, ya gode wa Oluremi Tinubu bisa tallafin da ta bayar, yana mai cewa motocin za su taimaka wajen ƙarfafa ayyukan matasan jam’iyyar da kuma shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Gwamna Abba Ya Amince Da Nadin Amirul Hajj Na Kano

Daga: Abdulmajid Habib Tukuntawa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince…

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Kudurinta Na Aiwatar Da Dokokin Sarrafa Filaye – Kwamishinan Filaye

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu  Kwamishinan Filaye da Tsare-tsaren Birane na Jihar Kano,…

Kwamandan Hukumar Civil Defense Ta Taya Gwamnatin Kano Alhinin Rasuwar ‘Yan Wasanninta

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Biyo bayan rasuwar ‘yan wasan Kano 22 da suka…

Direbobin NURTW Tashar Malam Kato Sun Yi Jimamin Rasa Babban Jigo A Kano

Daga: Ibrahim Sani Gama Kungiyar matuka motocin haya ta kasa reshen tashar malam…