Daga: Ibrahim Sani Gama

Kungiyar matuka motocin haya ta kasa reshen tashar malam kato, (bus 9) ta Mika sako ta’aziyyarta ga Gwamnatin jihar Kano da masarautar Kano musamman iyalan murigayin Alhaji Aminu Alhasan Dantata da sauran alummar jihar Kano, bisa rasuwa babanmu, kakanmu marigayi Alhaji Aminu Alhasan Dantata daya rasu yana da shekaru 94 da haihuwa.

Mataimakin kungiyar Alh. Samaila sale giredi me ya bayyana haka a yayin wata tattarawa da yayi tare da manema labarai a ofishinsa dake tashar malam kato a Nan jihar Kano.

Yace rasuwar Alhaji Aminu Alhasan Dantata, ba karamin rashi bane ga alummar jihar Kano da ma kasa baki daya.

 

Mataimakin shugaban kungiyar samaila giredi ya bayyana cewar, a madadin’yankungiyarsa ta NURTW dake tashar malam kato, suna baiwa iyalan murigayin da kungiyoyi na yankasuwa da sauran alummar jihar Kano ta”aziyya bisa wannan gagarumin Rashi da aka Yi Wanda ba za”a taba mantawa da shi ba.

 

Samaila sale yace Alh Aminu Alhasan Dantata ya taimakawa alummar jihar Kano, musamman yankasuwa da suke kokarin durkushewa bisa karayar Arziki da dai daikun mutane Wanda ba’a iya kirga su ba.

 

Samaila giredi yace, murigayin ya cibiyoyi da kamfanoni domin taimakawa alummar jihar Kano da sana’oin da za su dogara da kansu.

 

Dangane da masallatai da gidajen zama ya Gina ya bayar a matsayin sadakatul jariya,idon aka koma fannin harkokin ciyarwa Nan ma ba za’a manta da shi ba .

 

Alhaji samaila sale yayi Kira ga sauran masu hannu da shuni da su Yi koyi da hayan murigayi Allh Aminu Alhasan Dantata ta yin karamci ga sauran alummar jihar Kano da Kuma, makamantan abubuwa a kasashen ketare, Inda Kuma, yayi fatan Allah subahaanahu wata”ala ya jikansa da Rahman da iyayensu tare da sauran alummar Duniya baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Hukumar Tace Fina-finai Ta Jihar Kano Ta Dakatar Da Nuna Wasu Fina-finai Masu Dogon Zango 22

Daga: Muhammad Adamu Abubakar   A kokarinta na tabbatar da ana bin dokar…

Zamu Hada Kai Da Gwamnatin Jihar Kano Domin Bunkasa Harkokin Kasuwancin ‘Ya’yan Kungiyarmu

Daga: Ibrahim Sani Gama Kungiyar masu hada-hadar kasuwancin wayoyin hannu dake kasuwar…

Gwamnatin Jihar Kano Ta Yi Gangamin Yaki Da Cutar Zazzabin Sauro A Fadin Jihar

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi A ci gaba da kokarin kawar da cutar…

Gwamnan Filato Ya Yi Wa Jama’a Jawabi Daga Cikin Tanki Bayan Hari

Daga: Abdullahi Bashir Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya sanar da kafa dokar…