Daga: Shehu Suleiman Sharfadi

A ci gaba da kokarin kawar da cutar zazzabin cizon sauro, yaki da mace-macen mata masu juna biyu, da magance sauran cututtuka masu kashe yara, gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da shirin rigakafin cutar zazzabin cizon sauro na zamani na shekarar 2025 .

An gudanar da bikin kaddamar da shirin ne a ranar Talata a karamar hukumar Madobi, wanda mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo ya gabatar a madadin gwamna Abba Kabir Yusuf.

A nasa jawabin mataimakin gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na ba da fifiko kan harkokin lafiya da jin dadin mata da yara, inda ya bayyana su a matsayin kashin bayan al’umma mai albarka.

Mataimakin Gwamnan ya yi kira ga iyaye, masu kulawa, da sauran al’umma da su ci gajiyar ayyukan da ake yi da kuma taka rawar gani don samun ingantacciyar rayuwa.

Da yake jawabi tun da farko, Kwamishinan Lafiya, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya yabawa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa goyon bayan da take bayarwa wajen farfado da fannin kiwon lafiya.

Shima a nasa jawabin shugaban karamar hukumar Madobi Hon. Sulaiman Danazumi Kanwa, ya bayyana jin dadinsa da zabin Madobi a matsayin wurin kaddamar da taron, ya kuma yi alkawarin bayar da cikakken goyon baya ga majalisar.

Rahotanni sun nuna cewa, yaƙin kawar da cutar domin kiwon lafiya zai ƙunshi rarraba magungunan rigakafin zazzabin cizon sauro ga yara masu shekaru 3 zuwa watanni 59, rigakafi na yau da kullun, tallafin abinci mai gina jiki, sabis na kula da mata masu juna biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Sojojin Najeriya Sun Halaka ‘Yan Ta’adda Takwas a Borno

Daga: Hamza Garba Yakasai Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa dakarunta sun…

Shugabannin Jam’iyyar PDP Sun Kai Ziyara Helkwatar Hukumar Zabe Don Tattauna Kan Dokokinta

Daga: Abdullahi Muhammad Wani gagarumin kwamiti daga jam’iyyar PDP, karkashin jagorancin mukaddashin shugaban…

Muna Kara Mika Godiyar Mu ga Mai Girma Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf..Hon Isma’il Khalil Ja’en

A madadin Daliban makarantar Kano Film institute Tiga Muna Mika godia ga…

Gwamna Abba Ya Biya Kashi Na Hudu Na Bashin Fensho Ga Tsofaffin Ma’aikata a Jihar Kano

Daga: Sani Idris Maiwaya A ci gaba da nuna damuwa da kulawa ga…