Daga: Mas’ud Mato Garo
Mataimakin Gwamnan Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, ya ce zuba jari a fannin ilimi na taka muhimmiyar rawa wajen sauya rayuwar al’umma da ci gaban ƙasa.
Garo ya bayyana haka ne a bikin yaye ɗalibai 850 na Community College of Education, Kano, da Sanata Ibrahim Shekarau (Sardaunan Kano) ya ɗauki nauyin karatunsu, wanda aka gudanar a School of Arabic Studies (SAS), Kano.

Ya jaddada muhimmancin ilimantar da mata, yana mai cewa, “Idan ka ilimantar da mace, ka ilimantar da al’umma baki ɗaya.”
Mataimakin Gwamnan ya kuma yi kira ga ’yan siyasa da masu hannu da shuni da su yi koyi da gudunmawar Sanata Shekarau wajen bunƙasa ilimi.
Ya ce zai isar da buƙatar waɗanda suka kammala karatun ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, musamman kan batun samar musu da aikin yi.

A nasa jawabin, Sanata Shekarau ya yi kira ga gwamnatin Kano da ta samar wa makarantar filin dindindin domin ba ta damar faɗaɗa ayyukanta.