Daga: Mas’ud Mato Garo

Ita dai wannan karramawa ta wakana ne awajen bikin rantsar da sabbin shugabannin kungiyar a babban masallacin kasa dake Abuja ranar Larabar da ta gabata.

Da yake wakiltar gwamna Yusuf a wajen bikin, mataimakinsa Alhaji Murtala Sule Garo, ya karɓi lambar yabon a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kungiyar dai tayi la’akari ne da irin goyon bayan da gwamnatin jihar kano ke bai wa mahaddatan Alƙur’ani da ma makarantun Alƙur’ani a faɗin najeriya bakidaya.

Bugu da kari, mataimakin gwamnan Alh Murtala Sule Garo, ya miƙa lambobin yabo ga wasu mutane da sukayi fice wajen bayar da gudunmawar bunƙasa karatu da haddar Alƙur’ani a kasar nan.

Cikin mahalarta taron, akwai tsohon Gwamnan Kano,Malam Ibrahim Shekarau da Shugaban Hukumar kula da Ilimin Almajirai da Yaran da Basa Zuwa Makaranta ta Ƙasa, Dr Muhammad Sani Idris da dai sauran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Sakon Karrama Jagoran Kwankwasiyya, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, A Lokacin Zagayowar Ranar Haihuwarsa

Daga: Zakariyya Adam Jigirya A cikin wani sakon karramawa da aka gabatar…

Ya Zama wajibi su Girbi Abinda Suka Shuka a Karamar Hukumar Ungogo…. Nuhu Musa Muhammad Kunture

Daga: Sani Idris Maiwaya Nuhu Musa Muhammad. Dan Kishin Al’umma. Lokaci ya…

Shugaban K/H Birnin Kano, Salim Hashim, Ya Taya Al’umma Musulmi Murnar Shigowar Sabuwar Shekarar Hijira ta 1447

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu    Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kano, Alhaji Salim…

Hukumar Kula Da Kayayyakin Amfanin Gona Ta Shawarci Al’umma Su Tabbatar Da Ingancin Kaya

Daga: Muhammad Adamu Abubakar  Hukumar kula da kayayyakin amfanin gona da ake shigowa…