Daga: Mukhtar Yahaya Shehu
Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudurin ta na daukar matakin Doka ga wasu bata-gari da yanka filaye musamman a wuraren da ta yanka.
Kwamishinan kasa da tsare -tsare na jihar Kano Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar ne ya sanar da haka yayin holen wasu bata-gari gari ga manema labarai dq ake Zargi da yanka filaye a Gundutse Trailer Park da ke karamar hukumar Kura.

Kwamishinan ya ce ma’aikatar kasa da tsare -tsare ta dukufa wajen kawo karshen wadannan bata-gari da ke cin amanar gwamnati ta hanyar sake yanka filaye bayan ta kammala yanka su.
Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar ya kara da cewa Gundutse Trailer Park yanki ne mallakin gwamnatin jihar Kano da ta fitar da nufin wurin tsayawar manyan motocin daukar kaya da nufin rage cinkoson manywn motocin cikin birnin Kano zuwa kudancin kasar nan.
Kwamishinan ya jaddada kudurin ma’aikatar na cigaba da faraurar irin wadannan bata-gari musamman kasancewar a halin yanzu suka yanka irin wadannan filaye a Rimin Zakara.

Kwamishinan ya bayyana cewa a halin yanzu wadannan bata-gari da aka Kama za a Mika su ga kotu domin girbar abin da suka aikata.
Wadannan bata-gari da aka Kama da zargin yanka filayen su ne Muhammad Kabir Gaida Mai shekaru 57 da Kamilu Ilyasu Mai shekaru 55 da Kuma Mustafa Matazu da a yanzu ake nema bayan da ya tsere.
Idan za a iya tuna wa a karshen makon da ya gabata kwamishinan ma’aikatar kasa da tsare -tsare ta jihar Kano Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar ya jagoranci Kai sumamen Kama irin wadannan bata-gari da ke lalata Gadar watari da ke karamar hukumar Kumbotso suna yanka filaye ba bisa ka’ida ba a wurin inda aka Kama wasu daga cikin su aka Kuma gurfanar da su gaban kotu.