Daga: Jamila Suleiman Aliyu
A wani yunƙuri na ƙara ƙarfafa tsaro da tabbatar da zaman lafiya a Ƙaramar Hukumar Rimin Gado, an raba sabbin babura ga jami’an tsaro daban-daban domin inganta ayyukansu da kuma sauƙaƙa musu zirga-zirga yayin gudanar da aikin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Waɗanda suka amfana da wannan tallafi sun haɗa da jami’an Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC), Nigeria Immigration Service (NIS), Forest Security guard Service (FSS) da kuma Vigilante (VGN).
Da yake jawabi yayin rabon baburan, Shugaban Ƙaramar Hukumar Rimin Gado, Alhj. Muhammad Sani Salisu Jili, ya bayyana cewa samar da waɗannan babura wani ɓangare ne na ƙudirin gwamnatinsa na ƙarfafa hukumomin tsaro domin su samu damar gudanar da ayyukansu cikin inganci da saurin kai ɗauki ga al’umma.
Shugaban ya ce zaman lafiya shi ne ginshiƙin ci gaba, don haka gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tallafa wa jami’an tsaro da duk abin da zai taimaka musu wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya buƙaci jami’an da suka karɓi baburan da su yi amfani da su yadda ya kamata, su kula da su, tare da ci gaba da aiki cikin haɗin kai da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa Ƙaramar Hukumar Rimin Gado ta ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali.
A madadin hukumomin tsaron da suka amfana, wakilan jami’an sun bayyana farin cikinsu tare da miƙa godiya ga Shugaban Ƙaramar Hukumar bisa wannan gagarumin tallafi. Sun kuma yi alƙawarin ci gaba da aiki cikin ƙwarewa, aminci da sadaukarwa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Al’ummar Rimin Gado sun yabawa wannan mataki, suna mai bayyana cewa samar da irin waɗannan kayan aiki ga jami’an tsaro zai taimaka wajen ƙarfafa sintirin tsaro, saurin kai ɗauki a lokutan buƙata da kuma ƙara tabbatar da zaman lafiya a faɗin ƙaramar hukumar.