Daga: Mas’ud Mato Garo

Wani ayari na manyan jami’an Gwamnatin Jihar Kano ya kai ziyarar ta’aziyya jihar Sokoto domin nuna alhinin rasuwar Sardaunan Sokoto, Alhaji Abubakar Alhaji.

Mataimakin gwamnan kano Murtala Sule Garo ne ya jagoranci ayarin a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Sauran wadanda suka da fa masa baya ayayin ta’aziyar sun hadar da Sakataren Gwamnatin Jihar kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, Sarkin Rano, Mai Martaba Muhammad Isa Umar; Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar, Hon. Umar Haruna Doguwa; da Kwamishinar Al’adu da Yawon Buɗe Ido, Hajiya Aisha Lawan Saji, cikin wasu da dama.

Ayarin manyan jami’an na gwamnatin kano, ya isa har zuwa gidan iyalan marigayi Sardaunan Sokoto, inda ya isar da sakon ta’aziyyar Gwamnan kano Abba Kabir Yusuf ga iyalan marigayin.

Kaitsaye kuma ayarin sun ziyarci Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhd Sa’ad Abubakar na lll, domin isar da sakon ta’aziyyar Gwamna Yusuf gareshi inda sukayi addu’ar Allah ya jikan sa da rahama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Kungiyar sakwatawa mazauna jihar Kano ta jaddada kudirinta na tallafawa ‘ya’yan ta domin ganin sun dogara da Kawunansu.

Kungiyar sakwatawa mazauna jihar Kano ta jaddada kudirinta na tallafawa ‘ya’yan ta…

Tallafawa Maraya Sila Ce Ta Samun Makwabtaka Da Manzon Allah S.A.W A Aljannah

Daga: Musa Mudi Dawakin Tofa Malam Ali Yakubu Danjumma ne ya baiyana haka…

Gwamnatin Kano Ta Karɓi Rahoton Kammala Tsare-Tsaren Gina Kwalejin Fasaha a Gaya

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Gwamnatin Jihar Kano ta karɓi cikakken rahoton ƙarshe…

Kim Jong Un Ya Fara Nuna ’Yarsa Mai Shekara 13 A Matsayin Magajiyarsa

Daga: Abdullahi Bashir Rahotanni sun bayyana cewa shugaban Koriya ta Arewa, Kim…