Daga: Shehu Suleiman Sharfadi

Gwamnatin Jihar Kano ta karɓi cikakken rahoton ƙarshe daga kwamitin da ke kula da gina sabuwar Kwalejin Kimiyya da Fasaha a Gaya, lamarin da ke nuna ci gaba a yunkurin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na bunƙasa ilimi a jihar.

Mataimakin Gwamnan Kano kuma Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ne ya kai ziyara zuwa filin da aka ware domin gina makarantar, inda ya bayyana cewa dukkan shirye-shirye sun kammala kuma aikin zai fara nan ba da jimawa ba.

Yayin ziyarar tasa, Kwamared Gwarzo ya jinjinawa tarihinta Gaya a matsayin cibiyar ilimin addinin Musulunci da harkokin kasuwanci, musamman sana’ar narkar da ƙarfe. Ya ce zaɓin Gaya a matsayin matsugunin wannan makaranta alamar girmamawa ce da gwamnatin Kano ke nunawa wannan yanki mai dimbin tarihi.

Kwamared Gwarzo ya ƙara da cewa da zarar an fara aikin, ci gaba da arziki za su bayyana a yankin, inda ya bayyana cewa makarantar za ta jawo kafafen hada-hadar kuɗi, dakunan haya, gidajen abinci da kuma ƙanana da matsakaitan masana’antu a Gaya.

“Gina wannan Polytechnic zai buɗe ƙofofin cigaba a fannoni daban-daban, musamman tattalin arziki da walwalar al’umma,” in ji shi.

Ya kuma bukaci hadin kan shugabannin siyasa da na al’umma wajen marawa gwamnatin baya domin tabbatar da nasarar aikin.

Shugaban karamar hukumar Gaya, Hon. Mahmud Tajo Gaya, ya yi maraba da wannan ci gaba tare da bayyana goyon bayansa ga aikin, yana mai cewa ofishinsa zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin an kammala aikin cikin lokaci.

A lokacin ziyarar, tawagar ta kuma kai gaisuwa ga Sarkin Gaya, Alhaji (Dr.) Aliyu Ibrahim Gaya, a wani bangare na nuna haɗin kai tsakanin gwamnati da al’ummar yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Zamu Hada Kai Da Gwamnatin Jihar Kano Domin Bunkasa Harkokin Kasuwancin ‘Ya’yan Kungiyarmu

Daga: Ibrahim Sani Gama Kungiyar masu hada-hadar kasuwancin wayoyin hannu dake kasuwar…

Kano: Gwamnati Ta Jaddada Aniyar Cigaba da Yi wa Yara Allurar Rigakafi

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi  Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada kudirinta na ci gaba…

Hukumar Kare Hakkin Mai Siye Da Siyarwa:Mun Yi Nasarar Dakile Kayan Da Suka Lalace Da Dama A Jihar Kano

  Daga: Adamu Dabo Hukumar kare Hakkin Mai siye da siyarwa ta…

Bawa Mata Dama A Siyasa Shine Ginshikin Cigaban Al’umma

Daga: Kabir Getso Tsohuwar Babbar Daraktan Hukumar Kula da ‘yancin Mata ta Jihar…