Daga: Ibrahim Sani Gama
Kungiyar masu hada-hadar kasuwancin wayoyin hannu dake kasuwar Bata, Kano, ta bayyana kudirinta na hada kai da Ma’aikatar Kasuwanci da Ciniki ta Jihar Kano domin bunkasa harkokin kasuwanci a tsakanin ‘ya’yanta da sauran al’ummar jihar baki daya.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Sakatare Janar na kungiyar, Alhaji Aminu Uba Wada, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa dake Karami Plaza.

Alhaji Aminu Uba Wada ya bayyana cewa kungiyar ta dauki alkawarin amfani da duk wata hanya da ta dace domin kawo sababbin tsare-tsare da za su tallafa wa ci gaban kasuwancin wayoyin hannu a jihar.
“Lokaci yayi da ya kamata masu harkar sayar da wayoyi su fahimci cewa shugabanci ba na mallaka bane, yana da matukar muhimmanci a samu shugabanci nagari wanda za a gudanar da shi cikin gaskiya da adalci, ba kamar yadda wasu suka saba a baya ba,” inji Sakataren.
Ya kuma bayyana cewa shugabancin da ake yi a halin yanzu shugabanci ne na rikon kwarya, wanda da zarar lokacin zabe ya yi, za a gudanar da sahihin zabe cikin gaskiya domin bai wa kowa dama.

Sakataren ya ja hankalin al’umma cewa shugabanci ba hanya ba ce ta tara dukiya ko azurta kai, amma hanya ce ta sadaukarwa da hidimtawa ga jama’a.
“A baya wasu shugabannin sun dauki mulki a matsayin gadonsu, amma yanzu al’umma sun waye, suna da damar fadin albarkacin bakinsu,” inji shi.
Alhaji Aminu Uba Wada ya kuma yi kira ga dukan ‘ya’yan kungiyar da su mara wa shugabanni baya tare da ba su hadin kai domin tabbatar da shugabanci na gaskiya da zai amfanar da kowa.
Daga karshe, ya tabbatar da cewa kungiyar za ta baiwa Gwamnatin Jihar Kano goyon bayan da ya kamata domin ciyar da harkokin kasuwanci gaba, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen sa jihar Kano ta zama daya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci a nahiyar Afirka.
