Daga: Kabir Getso

Hukumar Bunƙasa Harkokin Noma Da Samar Da Abinci Na Zamani Ta Jihar Jigawa (JATA) ta karyata jita-jitar da ake yaɗawa cewa ana sayar wa manoman jihar kayayyakin noma daidai da farashin kasuwa, tana mai bayyana cewa ana sayar da su ne cikin rangwamen farashi domin tallafa wa manoma.

Daraktan Janar Na Hukumar, Dr. Saifullahi Umar, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke Birnin Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.

Ya ce wasu na yaɗa jita-jitar cewa gwamnatin jihar ta tsaurara farashin kayayyakin noma, yana mai bayyana wannan ikirari a matsayin “kanzon kurege” wanda ba shi da tushe balle makama.

Dr. Saifullahi Umar ya buƙaci al’ummar jihar da su yi watsi da irin waɗannan rahotanni, yana mai jaddada cewa gwamnatin Jihar Jigawa, ta hannun JATA, ta tanadi kayayyakin noma cikin rangwamen farashi domin ƙarfafa manoma da bunƙasa harkokin noma a faɗin jihar.

Daraktan Janar ɗin ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar Jigawa da su ci gaba da bai wa Gwamna Malam Umar Namadi cikakken goyon baya da haɗin kai domin samun damar aiwatar da sabbin tsare-tsare da ayyukan raya ƙasa da gwamnatin jihar ke ƙaddamarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Zamu Tsaya Ysayin Daka Domin Ganin An Zabi Shuwagabanni Nagari A Zabe Mai Zuwa 

Daga: Abdulmajid Habib Isah Tukuntawa Jam,iyar PRP Mai alamar Dan mabudi ta gabatar…

Ku Zama Jigo Wajen Gina Dimokuraɗiyyar Nijeriya: Kiran Gwamnatin Tarayya Ga ‘Yan Jarida.

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Gwamnatin Tarayya ta magantu a yayin da ta…

Hukumar Kare Hakkin Mai Siye Da Siyarwa:Mun Yi Nasarar Dakile Kayan Da Suka Lalace Da Dama A Jihar Kano

  Daga: Adamu Dabo Hukumar kare Hakkin Mai siye da siyarwa ta…

Matasan Rimin Gado Sun Zargi Barau Da Siyen Kuri’a, Sun Bukaci Gaskiyar Tallafi

Daga: Ibrahim Sani Gama Shugaban kungiyar matasan ‘yan siyasa a karamar hukumar Rimin…