Daga: Ibrahim Sani Gama

Shugaban kungiyar matasan ‘yan siyasa a karamar hukumar Rimin Gado ya bukaci Sanata Barau I. Jibrin da ya mayar da hankali wajen tallafawa al’ummar mazabarsa ba tare da jiran lokacin zabe ba.


Shugaban kungiyar, Aminu Abdullahi Sidi (Juji), ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai. Ya ce matasan yankin na ganin cewa rabon kudi da ake yi a lokacin siyasa ba ya wakiltar ingantaccen tallafi, yana mai cewa “masoya na gaskiya ba a sayensu da kudi.”


Ya zargi Sanatan da fito da wani tsari na tara mutane tare da raba musu kudi domin jawo hankalinsu gabanin zabe, yana mai cewa wannan hanya ba za ta haifar da nasara ba, domin al’umma sun fara fahimtar yadda ake tafiyar da siyasa.

A cewarsa, maimakon hakan, ya kamata Sanatan ya koma ga mutanen da suka mara masa baya tun farko, wadanda a cewarsa yanzu suna cikin halin kunci da talauci.

Kungiyar ta kuma bukaci duk wanda aka gayyata domin karbar irin wannan tallafi da ya karba a matsayin hakkinsa, amma ta gargadi jama’a da kada su yarda a yaudare su da irin wadannan dabaru na siyasa da ba su da dorewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Gwamnatin Kano Na Cigaba Da Yiwa Ilimi Gata Don Kyautata Rayuwar Al’umma – Hon. Rabiu

Daga: Kabir Getso Gwamnatin Kano na ciga ba da yiwa ilimi gata…

Jibrin Kofa Ya Jagoranci Kaddamar da Sabon Rukunin Gidaje a Abuja

Daga: Zakariyya Adam Jigirya Abuja – A wani babban taron da ya…

Garo Ya Kama Aiki, Ya Yi Alkawarin Adalci Da Kyakkyawan Jagoranci

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Sabon mataimakin gwamnan jihar Kano, Alhaji Murtala Sule…

Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano, Gawuna, Ya Sauya Jam’iyya

Daga: Hamza Musa Yakasai Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Nasir Yusuf Gawuna, ya…