Daga: Abdullahi Bashir
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC), ta dakatar dan asusun gwamnatin jihar Osun da ke banki, kwanaki 10 kafin gudanar da zaben gwamna wanda zai gidana a ranar 15 ga Agusta, 2026.
An gano cewa asusun da aka dakatar shi ne ake amfani da shi wajen biyan albashin ma’aikatan gwamnati. Hukumar ta sanya masa matsayin dakatar da duk wata mu’amalar fitar da kuɗi daga asusun (Post No Debit) wanda ke nufin ba za a iya fitar da kudi daga ciki ba.
Wannan mataki ya zo ne ‘yan sa’o’i kadan bayan Gwamna Ademola Adeleke ya bayyana cewa EFCC na shirin dakarar da asusun jihar da na manyan jami’an gwamnati.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da wayar da kai na jihar, Hon. Kolapo Alimi, ya fitar a ranar Laraba, gwamnan ya bayyana wannan yunkuri a matsayin “yunkurin dagula ayyukan gwamnati da gangan domin kawo cikas kafin zabe.”
Gwamna Adeleke ya ce, gwamnatinsa za ta dauki matakin da ya dace na doka don tabbatar da cewa an cire dakatarwar da aka yi domin kada a sha wahalar biyan albashi.
Hukumar EFCC kuma har yanzu ba ta fitar da wata sanarwa ta hukuma ba dangane da lamarin.