Daga: Zakariyya Adam Jigirya
A cikin wani sakon karramawa da aka gabatar a ranar Talata, Alhaji Mustapha Hamza Buhari Bakwana, wani jigo ne a kungiyar Kwankwasiyya kuma tsohon mai ba da shawara ga gwamnan Kano, ya bayyana tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, a matsayin jagora mai hangen nesa a siyasar arewacin Najeriya.

A cikin sakon, Bakwana ya bayyana Kwankwaso a matsayin jagora mai kishin kasa wanda burinsa a koyaushe shine ci gaban yankin Arewacin Najeriya da ma kasar baki daya. Ya jaddada cewa Kwankwaso, wanda ya cika shekaru 69 a ranar 21 ga Oktoba, yana daya daga cikin manyan shugabannin da suka yi fice wajen samar da ci gaba, musamman a fannonin ilimi da kiwon lafiya a jihar Kano da Najeriya baki daya.

Bakwana ya bayyana cewa Kwankwaso yana cikin jagororin da ke baiwa kasar gudunmawa mai girma ta hanyar gudanar da shirye-shiryen ci gaba da suka shafi al’umma. Ya kara da cewa, “A yau, muna karrama shugaban da yake da hangen nesa wanda burinsa shine cigaban al’umma da daukar matakin cigaban na kasa da shi. Kamar yadda muka shaida wannan rana mai cike da tarihi, Allah ya sa shekara mai zuwa ta cika domin cimma manufar mu, ta jawo al’ummarmu zuwa ga mafi kyawu a tarihi.”
A cikin wannan karramawar, Bakwana ya yi addu’ar Allah ya kara wa Kwankwaso lafiya da tsawon rai, yana mai fatan ganin ci gaban shugabancin Kwankwaso ya ci gaba da zaburar da al’umma.
“Allah Madaukakin Sarki ya baiwa jagoranmu Engr. Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso tsawon rai, arziki, da shiriyar Ubangiji,” in ji Bakwana.
Bayan haka, Bakwana ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa jagorancin gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, zai kai jihar Kano ga babban birni mafi girma a kasar nan, yana mai bayyana gamsuwa da yadda gwamnatin jihar Kano ke aiwatar da ayyukan ci gaban ababen more rayuwa.
Mustapha Bakwana ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano tana tafiya daidai da manufar ci gaba da kawo sauyi mai amfani ga al’umma, yana mai jaddada cewa tabbas wannan ci gaban zai canza fasalin jihar Kano zuwa mafi kyawun tarihi.
