Daga: Ibrahim Sani Gama
Mutane 176 da aka sace a hare-haren da ‘yan ta’adda suka kai kauyukan Woro da Nuku da ke Ƙaramar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara a ranar 3 ga Fabrairun shekarar nan, sun samu ‘yanci bayan sun shafe kusan wata shida a hannun masu garkuwa da su.
Gwamnatin Jihar Kwara ta tabbatar da sakin mutanen, inda ta yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki kan rawar da suka taka wajen ganin an kubutar da su.

Yawancin wadanda aka sace mata da kananan yara ne. Sun shiga hannun ‘yan ta’addar ne bayan mamayar da aka kai wa kauyukan na Woro da Nuku, inda aka kashe mutane da dama tare da kona gidaje.
Har zuwa lokacin fitar da wannan rahoto, ba a bayyana yadda aka samu sakin mutanen ba, kuma ba a tabbatar ko an biya kudin fansa ba.