Shugaban Hukumar Karota a Jihar Kano Alhaji Faisal Mahmud Kabir, ya bayyana Cewar nan ba da jimawa ba hukumar sa za ta Gayyaci Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa NDLEA domin tantan ce Ma’aikatan Hukumar, da nufin gano wadanda suke ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a Hukumar ta Karota

 

Mahmud Kabir ya bayyana haka ne a lokacin da kwamandan Hukumar NDLEA na Jihar Kano, Dahiru Yahaya Lawal, ya kai masa ziyara a ofishin Hukumar ta Karota

 

Inda Shugaban na KAROTA ya ce tantancewar da za’a yiwa Jami’an nasu ya zama wajibi domin kawar da duk masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi daga cikin ma’aikatan hukumar Karotan

 

Faisal Mahmud Kabir ya Kuma tabbatar da cewa KAROTA za ta ci gaba da yin aiki tare da NDLEA wajen yaki da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi musamman tsakanin matasa, wadanda ya ce su ne ginshikin makomar ƙasa da al-umma.

 

Da yake nasa Jawabin Babban Kwamandan NDLEA na Kano, Dahiru Yahaya Lawal, ya ce Sun Kawo Ziyarar tasu ne zuwa shalkwatar KAROTA Domin ƙarfafa kyakkyawar alaka ta Aiki tsakanin Hukumar tasu da Kuma Hukumar ta KAROTA.

 

Domin Samun Damar Gudanar da Aiki Yadda ya Kamata Bisa Tsari, yayin Ziyarar Kwamandan NDLEA din na Tare Manyan Jami’an Hukumar da Sukayi Masa Rakiya Zuwa Hukumar ta Karotan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Kwamatin Tsaro na Majalisar Karamar Hukumar Dala ya Haramta Dunkannin Wani Taron Gangi, ko kidan Tauri Dama Duk Wani taro akan hanyar da Al’umma Ke wucewa a Fadin Karamar Hukumar Dala

Kwamatin Tsaro na Majalisar Karamar Hukumar Dala ya Haramta Dunkannin Wani Taron…

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Watsi Da Abincin Da Ake Bai Wa Alhazan Najeriya A Hajji

Daga: Abdullahi Bashir Hukumar Alhazai ta Kasa, National Hajj Commission of Nigeria…

Sanata Barau Jibrin Zai Raba Wa Al’ummar Kano Ta Arewa Naira Miliyan 134.9 A Matsayin Kyautar Barka Da Sallah

Daga: Abdullahi Bashir Al’umma maza da mata na yankin Kano Ta Arewa suna…

Dandazon al’umma sun tarbi gwamnan Kano biyo bayan dawowarsa daga kasa Mai tsarki

Daga: Adamu Dabo   A yau laraba dubban al’ummar jihar Kano daga…