Daga: Abdullahi Bashir

Hukumar Alhazai ta Kasa, National Hajj Commission of Nigeria (NAHCON), ta yi watsi da wasu abinci da aka bai wa alhazan Nijeriya a ƙasar Saudi Arabia bisa zargin karya ƙa’idojin lafiya da tsarin tattara abinci.

A wata sanarwa da mahukuntan hukumar suka fitar, NAHCON ta bayyana cewa hukumomin lafiya na Saudiyya na ci gaba da sanya ido sosai kan bin ƙa’idojin tsaron abinci yayin gudanar da aikin Hajjin bana, musamman saboda yanayin zafi da ake fama da shi a ƙasar.

Hukumar ta ce wasu abincin dare da aka raba wa alhazai a daren Talata, 27 ga Mayu, 2026, ba su cika ƙa’idojin da aka shimfiɗa kan yadda ake sarrafa da kuma tattara abinci ba, lamarin da ya sa aka yi gaggawar ƙin karɓarsu tare da haɗin gwiwar jami’an Saudiyya.

Domin rage wa alhazan da abin ya shafa raɗaɗi, kamfanin da ke kula da hidimar abinci ya samar musu da wasu kayan marmari da abinci mai sauƙi, yayin da mambobin kwamitin gudanarwar NAHCON suka zagaya domin yi wa jami’an jihohi da masu kula da alhazai bayani kan lamarin.

A wani mataki na nuna tsattsauran ra’ayi wajen kare jin daɗin alhazai, shugaban hukumar NAHCON, Ismail Abba Yusuf, ya umarci kwamitin tsaro na hukumar da ya binciki masu samar da abincin da kuma waɗanda suka taimaka wajen bayar da kwangilar.

Haka kuma shugaban ya ba da umarnin gudanar da wani bincike na daban kan wasu kamfanonin yawon Hajji da ake zargi da kawo alhazai fiye da adadin da suka yi rajista da kuma anfani da wasu alhazai ba tare da saninsu ba.

NAHCON ta ce duk wani kamfani da aka samu da laifi bayan kammala bincike zai fuskanci hukunci, ciki har da soke lasisin gudanar da aiki.

Hukumar ta kuma bayyana cewa tuni aka fara shirye-shiryen mayar wa alhazan da abin ya shafa kuɗaɗensu.

A ƙarshe, hukumar ta gode wa alhazan bisa haƙurin da suka nuna tare da tabbatar musu da ci gaba da kula da jin daɗinsu da tsaronsu a duk lokacin gudanar da aikin Hajji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

‘Yar Kasuwa Ta Samu Kyautar N500,000 Bayan Mayar Da N1m Da Ta Tsinta A Jos

Daga: Abdullahi Bashir Wani fitaccen ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa, Ambasada Abubakar…

Gwamna Abba Ya Karɓi Baƙuncin Tawagar Gwamnatin Jihar Borno

Daga: Sani Idris Maiwaya Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir…

Jaridar BusinessDay ta karrama Gwamnan Jihar Kano da lambar yabon Business Governor of the Year.

Daga Mas’ud Mato Garo Mataimakin gwamnan kano Murtala Sule Garo ne ya…

Kungiyar Matasa Masu Neman Aikin Koyarwa Ta Yabawa Gwamnatin Kano Kan Tsarin Jarabawa

Daga: Ibrahim Sani Gama Kungiyar matasan da suka rubuta jarrabawar neman aikin koyarwa…