Daga: Kabir Getso
Gwamnatin Kano na ciga ba da yiwa ilimi gata don kyautata Rayuwar al’umma -Hon Rabi’u Saleh Liliko
Babban Sakataren Hukumar kula da Malaman makarantun Sakandire na Jihar Kano.
A Makon da ya gabata ne Gwamnatin Jihar kano ta kaddamar da daukan malaman makaranta sama da Dubu 4 a jihar don cigaba da inganta Sha’anin ilimi a Jihar.

Babban Sakataren Hukumar kula da Malaman makarantun Sakandire na Jihar Kano Hon Rabi’u Saleh Liliko ya bayyana kokarin wannan gwamnati a Harkar Ilimi a lokacin da yake ganawa da manema Labarai a ofishinsa.
Yace babu shakka Gwamnatin Jihar Kano karkashin Gwamna Engr Abba Kabir Yusif yana namijin kokari wajen sauke nayin da ya rataya a wuyansa. “Al’umma shaida ne irin yadda Gwamna ya ware kaso mafi tsoka ga ilimi a kasafin kudi wanda ya kara tabbatar da kokarin Gwamna wajen cika alkawarukan da ya dauka tun a lokacin zabe” inji shi.
Hon Rabi’u Saleh Liliko Gwarzo yayi kira ga dukkannin Malaman da suka samu wannan dama ta samun aiki da su rike amana da aiki tukuru don sauke nauyin da aka dora masu.

Jarirjewa wajen aiki kula da ka’idojin aikin da kuma zuwa aikin akan lokaci na daga cikin abubuwan da yakamata su kula don cigaban aikin nasu da al’umma baki daya.
Da aka tambayeshi game da batun wasu manyan makarantun da aka rufe tun lokacin baya, yace “Tuni Shiri yayi nisa wajen farfado da wadancan makarantun tare da bude su acigaba da koyo da koyarwa cikin tsari fiye da baya.
Hon Rabi’u Saleh ya shawarci daukacin al’ummar Jihar Kano da su cigaba da bawa Gwamnatin Jihar Kano cikakkencikakken hadin kai da goyon baya don bunƙasa harkokin ilimi da sauran abubuwan more rayuwa a Jihar Kano.