Daga: Kabir Getso

Gwamnatin Tarayya ta sahale wa Kwalejin Ilimi ta Kasa Reshen Karamar Hukumar Bichi yin kwasa-kwasan digiri domin kyautata ingancin ilimin al’umma dake fadin kasar nan.

A sanarwar da Jami’ar Yada Labarai ta Karamar Hukumar Bichi, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta raba wa Manema Labarai, Shugaban kwalejin, Dakta Bashir Sabo Abubakar ne ya bayyana haka a yayin tattaunawarsu da Manema Labarai a ofishinsa na FCE Technical dake Karamar Hukumar Bichi.

Da yake jawabi, Dakta Bashir Sabo Abubakar, ya bayyana wannan cigaba da aka samu ta fuskar alakanta kwasa-kwasan da ake yi tsakanin jiya da yau a FCE Technical Bichi, wanda a halin yanzu ake koyar da sama da kwasa-kwasai ashirin (20) a cikinta.

“A baya duk wani NCE program da ake yi a Nijeriya muna yi, amma mun dade muna ba da digiri ta hadin gwiwar Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa Bauchi da Jami’ar Jos. Yanzu kuma a shekarar 2023 da ta gabata, gwamnatin Alhaji Bola Ahmad Tinubu ta sahale wa kwalejoji yin digiri a karkashin gashin kansu ba tare da hadin kai da jami’o’i ba, yanzu haka muna sikirinin duk wanda yake da maki dari da hamsin (150) a UTME ya nemi girin kad ya canja ya zo FCE Bichi.”

Kazalika, Shugaban Kwalejin Ilimin, ya shelanta jama’a su ne hujja da madogarar tabbatar da gagarumar nasarar da wannan makaranta ta rabauta da shi, musamman idan aka yi la’akari da a matakin yanzu ita ce kwalejin da tafi kowace kwaleji yawan dalibai a fadin kasar nan.

Ya ce, daga cikin manyan nasarorin da makarantar ta samu, sun gyara dakunan kwanan dalibai wadanda sama da shekaru talatin (30) a baya ba a gyara su ba, haka sun samar da dakunan karatun daukar darasi tare da gyaran ofisoshin malamai. Sannan sun inganta bangaren karatu ta hanyar shirya tarukan kara wa juna ilimi domin sanin makamar aikinsu da dabarun koyo da kuma koyarwa.

Ya yaba wa Shugaban Karamar Hukumar Bichi, Alhaji Hamza Sule Mai Fata bisa taimakonsa ga cigaban ilimin yankin, ya kuma bayyana irin gagarumar gudunmawar da Gwamnatin Kano, karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf take bayar wa a bangaren ilimi, tare da jinjina wa Dan Majalisar Tarayya mai Wakiltar Bichi, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar bisa daukar nauyin karatun dubban jama’a da ya sa a gaba domin kyautata rayuwarsu.

A karshe, ya ja hankalin al’uma game da koyi a kan al’amuran gina al’uma, musamman bangaren ilimi gishirin rayuwa.

“Ko nauyin mutum daya za ka iya dauka, to ka dauka domin duk wanda zai fara amfanar ilimi wanda yake da shi ne a karan-kansa, idan ka bar yaro ba ilimi ku zai fara damu a unguwa. Duk yadda za a yi, a kwamitince ne, a unguwa ne, ‘yan majalisa ne, duk wanda yake da wata dama dai ya taimaka a je a yi ilimi da koyon sana’a domin ta wannan hanyar al’uma take samun zaman lafiya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Fiye da Matasa 6,000 da Masu Horarwa Sun Yi Rijista Don Gasar Matasa ta Kasa a Asaba

Daga: Zaharaddeen Saleh Hukumar wasanni ta Kasa ta tabbatar da cewa jimillar ‘yan…

Gwamna Abba Ya Ƙaddamar da Gangamin Rigakafin Masassara a Tofa — Mataki Na Farko a Nahiyar Afirka

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya…

Ku Zama Jigo Wajen Gina Dimokuraɗiyyar Nijeriya: Kiran Gwamnatin Tarayya Ga ‘Yan Jarida.

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Gwamnatin Tarayya ta magantu a yayin da ta…

Kungiyoyin Matuka Motocin Kurkura Da Na Manyan Motoci Sun Yi Alwashin Tallafawa Tsaftace Muhalli

Daga: Ibrahim sani Gama Kungiyar matuka motocin korkura ta jihar Kano da…