Kwamatin Tsaro na Majalisar Karamar Hukumar Dala ya Haramta Dunkannin Wani Taron Gangi, ko kidan Tauri Dama Duk Wani taro akan hanyar da Al’umma Ke wucewa a Fadin Karamar Hukumar Dala
Shuganban Karamar Hukumar Dala Alhaji Suraj Ibrahim Imam Shine ya Bayyana hakan Jim Kadan bayan Kammala Zama da Kwamatin Tsaro na Yankin Karamar Hukumar ta Dala.
Suraj Imam yace wannan Mataki ya biyo bayan Samun Wani fadan Daba Daya kawo hargitsi a Karamar Hukumar ta Dala.
Yana Mai Cewar Daga yau duk Wani da aka Samu da Karya wannan Doka to Tabbas Zai fuskanci fushin Hukuma.
Taron Kwamatin Tsaron ya hadar da Jami’an Tsaro na Yansanda da Jami’an Tsaro shige da Fice, harma da Jami’an Tsaro na Civil Defence.
Wanda aka Gudanar a Karamar Hukumar Dala , Bisa kulawar Shugaban Karamar Hukumar Dala da Kuma hakimin Gobirawa