Daga: Ibrahim Sani Gama

Kungiyar ‘yan kasuwar kayayyakin masarufi ta kasa, reshen jihar Kano, ta bukaci Gwamnatin jihar Kano da ta tallafa mata da jari domin kara habaka ayyukanta da kuma ci gaban ‘yan kasuwar.

Mataimakin shugaban kungiyar, Alhaji Auwalu Allah Ya Tsare, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke kasuwar Singa.

Alhaji Auwalu ya jaddada kudirin kungiyar na marawa Gwamnatin jihar Kano baya a fannoni daban-daban, yana mai yabawa gwamnatin karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf kan yadda take aiwatar da manyan ayyukan raya kasa a sassan jihar.

Ya ce duk wanda ya duba irin ayyukan da gwamnatin ke gudanarwa zai tabbatar da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya cika alkawuran da ya daukar wa al’ummar Kano na samar da ayyukan da za su bunkasa tattalin arzikin jihar.

A sakamakon haka, ya yi kira ga Gwamnatin jihar Kano da ta tuna da kungiyar Kwankwasiyya Singa Market, duba da rawar da take takawa wajen ci gaban tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga matasa a fadin jihar.

Haka zalika, Auwalu ya bayyana bukatar kungiyar ta samu sahalewar hukuma (notice) da za ta ba ta damar shiga cikin shirye-shiryen Gwamnati kamar yadda sauran kungiyoyi ke samu, domin kada a barsu a baya.

Ya kara da cewa kokarin da Gwamnatin jihar Kano ke yi na raya kasa ya cancanci yabo, yana mai rokon gwamnati da ta yi duba na tsanaki kan gudunmawar da kungiyar Kwankwasiyya Singa Market ke bayarwa wajen ci gaban jihar.

A karshe, ya ce lokaci ya yi da ya dace Gwamnatin jihar Kano ta tallafa wa kungiyar da jari, musamman ganin yadda take taimakawa wajen daukar marasa aikin yi tare da basu damar dogaro da kawunansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Masu Buƙata Ta Musamman A Kano Sun Koka Kan Rashin Samun Tallafin Gwamnati

Daga: Ibrahim Sani Gama Shugabancin Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa Masu Buƙata ta Musamman ta…

Gwamnatin Kano Ta Taya Daukacin Al’ummar Jihar Murnar Barka Da Sallah

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, tare…

Yin Shugabanci Nagari Da Gudanar Da Ayyuka Masu Ma’ana – Gawuna

Daga: Zakariyya Adam Jigirya Gawuna ya karɓi ragamar shugabancin hukumar gudanarwar bankin…

Tinubu Ya Taya Rediyon Tarayya Murnar Cika Shekaru 75, Ya Jaddada Muhimmancinta A Kasa

Daga: Zakariyya Adam Jigirya Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya mahukunta…