Daga: Shehu Suleiman Sharfadi

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, tare da mataimakinsa, Alhaji Murtala Sule Garo, da sauran manyan jami’an gwamnati, sun taya al’ummar Musulmi a Jihar Kano da ma fadin kasar nan murnar bikin Babbar Sallah ta shekarar 2026.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne jim kadan bayan gudanar da sallar Idi raka’a biyu a filin Idi da ke Kofar Mata a birnin Kano.

Gwamnan ya bayyana Eid-el-Kabir a matsayin wata babbar ibada da ke koyar da darussan sadaukarwa, biyayya, hakuri da tausayi, tare da kira ga Musulmi da su ci gaba da aiki da koyarwar bikin a rayuwarsu ta yau da kullum.

Ya kuma bukaci al’ummar jihar da su gudanar da bikin Sallah cikin lumana tare da kaucewa duk wani abu da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya, yana mai jaddada muhimmancin soyayya, hakuri da mutunta juna a tsakanin al’umma.

Haka zalika, Gwamna Yusuf ya yi kira ga iyaye da masu kula da yara da su ja kunnen ‘ya’yansu kan kaucewa halayen ganganci yayin bukukuwan Sallah, tare da gargadin matasa da su kasance masu bin doka da oda da kuma bai wa jami’an tsaro hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya.

Gwamnan ya kuma bukaci al’umma da su yi amfani da wannan lokaci na bukukuwa wajen yi wa Kano da Najeriya addu’o’in zaman lafiya, hadin kai da ci gaba mai dorewa.

Ya sake tabbatar da kudirin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar al’umma tare da tabbatar da ci gaba mai dorewa a fadin jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma taya Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima da sauran gwamnoni a fadin kasar nan murnar bikin Eid-el-Kabir.

A cikin muhimman abubuwan da suka gudana yayin bikin Sallah, Gwamnan ya kai ziyarar gaisuwar Sallah zuwa Majalisar Masarautun Kano da aka fi sani da Gidan Shattima, kamar yadda al’ada ta tanada bayan idar da sallar Idi.

Daga bisani, Gwamna Yusuf ya ziyarci makabartar Dandolo inda ya yi addu’ar Allah ya jikansa marigayi Alhaji Kabir Yusuf, tare da yi wa sauran mamatan Musulmi a jihar da kasa baki daya addu’ar samun rahama.

A karshe, Gwamnan ya yi wa al’ummar Musulmi fatan gudanar da bikin Eid-el-Kabir cikin zaman lafiya, nasara da farin ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Sanata Barau Jibrin Zai Raba Wa Al’ummar Kano Ta Arewa Naira Miliyan 134.9 A Matsayin Kyautar Barka Da Sallah

Daga: Abdullahi Bashir Al’umma maza da mata na yankin Kano Ta Arewa suna…

Kwamandan Hukumar Civil Defense Ta Taya Gwamnatin Kano Alhinin Rasuwar ‘Yan Wasanninta

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Biyo bayan rasuwar ‘yan wasan Kano 22 da suka…

Zamu Karbi Shawarwarin Hukumar Kiyaye Hadurra Domin Dakile Yawaitar Hadurra A Gadar Dakatsalle

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Gwamnatin jihar Kano ta bukaci hukumar kiyaye hadurra…

Gwamnati Ta Taka Mahimmiyar Rawa A Fannin Harkokin Ilimi – Mal. Muhammad Yakubu

Daga: Ibrahim Sani Gama Makarantar raudatul Janna Islamiyya dake Karamar Hukumar ungogo…