Daga: Shehu Suleiman Sharfadi
Gwamnatin jihar Kano ta bukaci hukumar kiyaye hadurra ta kasa ta yi bincike game da musabbabin yawaitar hadurra a gadar dakatsalle shekara da shekaru.
Mataimakin gwamnan jihar Kano a madadin gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya furta hakan yayin da ayarin hukumar kiyaye hadurra ta kasa karkashin jagorancin malam shehu Muhammad min wanda kwamandan shiyya na hukumar Ahmed umar suka kawo masa ziyarar ta’aziyya.

Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya nuna musu cewar gwamnatin jihar Kano a shirye take da ta karbi dukkan wasu shawarwari da suka shafi hanyoyin da suke jihar Kano da ma kasa baki daya.
Shima anasa bangaren kwamandan shiyya Ahmed Umar ya bayyana cewar sun zo Kano ne domin yin taaziyyar rasuwar yan wasan motsa jiki da hatsarin mota ya rutsa dasu a kan hanyar su ta dawowa gida daga jihar Ogun.
Ya kuma baiwa gwamnatin jihar Kano tabbacin bincikar musabbabin yawaitar hadurra a wannan gadar ta Dakatsalle.
Wakilinmu ya ruwaito cewar, kwamandan shiyyar ya samu rakiyar kwamandojin jihohin Kano, Jigawa, Katsina da Kaduna.