Daga: Shehu Suleiman Sharfadi

Biyo bayan rasuwar ‘yan wasan Kano 22 da suka dawo daga gasar wasannin motsa jiki na kasa da aka kammala kwanan nan a garin Abeokuta na jihar Ogun, gwamnatin jihar Kano ta ci gaba da karbar ta’aziyya.

A yau ne mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya karbi bakuncin tsohon gwamnan jihar, Sanata Malam Ibrahim Shekarau, wanda ya jagoranci ayarin jam’iyyar PDP.

Sanata Shekarau ya yabawa gwamnatin jihar bisa hanzarin da ta yi bayan afkuwar hatsarin, musamman yadda ta bayar da tallafin kudi da abinci ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu. Ya kuma, yabawa mataimakin gwamnan bisa jajurcewarsa wajen kulawa da lafiyar wadanda suke raye daga cikin yan wasan.

Ya kuma jaddada cewa, kamata ya yi siyasa ta zama dandalin hadin gwiwa maimakon gaba da juna, inda ya kara da cewa, “A halin yanzu gwamnatin NNPP ce ke jagorantar jihar Kano, kuma hakki ne na hadin gwiwarmu mu tallafa ma na.

Hakazalika, shugaban hukumar wasanni ta kasa, Shehu Dikko, ya jagoranci wani ayari a madadin shugaba Bola Ahmed Tinubu domin mika ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar Kano, musamman ma domin su jajantawa iyalan su.

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kuma kai ziyarar jaje ta hannun Kwanturolan Hukumar Kwastam na yankin Kano/Jigawa, Kwanturola Dalhatu Abubakar, wanda ya wakilci Shugaban Kwanturola Janar na Hukumar inda ya bayyana mutuwarsu a matsayin babban rashi ga kasa da kuma bangaren wasanni.

A wani labarin kuma, kungiyar kwadago ta Najeriya NLC Council Kano karkashin jagorancin mataimakin shugabanta, Kwamared Auwalu Muhammad Yakasai, ita ma ta ziyarci gwamnati domin yin jaje. Da yake magana a madadin shugaban kungiyar, ya bayyana mutuwarsu a matsayin babban rashi inda yayi musu addu’ar samun rahamar ubangiji.

Da yake mayar da martani a madadin gwamnati da iyalan wadanda suka rasu, Mataimakin Gwamna, Kwamared Aminu Abdussalam ya nuna matukar jin dadinsa kan yadda wasu mutane suka nuna kauna da hadin kai.

Wakilinmu, ya ruwaito cewa, jami’an gwamnati daban-daban na zuwa domin yin ta’aziyya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Kudirin Hada Gwiwa da Kungiyar Injiniyoyi ta Kasa Don Tabbatar da Ingancin Ayyuka

Daga: Ibrahim Sani Gama Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana kudirinta na ci…

Sakon Barka da Sallah daga Dr. Nasiru Yusuf Gawuna

Daga: Zakariyya Adam Jigirya Shugaban Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar Bayero Kano, kuma Shugaban…

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kaddamar da Rabon Transformers 500 Ga Kananan Hukumomi 44 a Kano

Daga: Sani Idris Maiwaya KANO – Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir…

Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano, Gawuna, Ya Sauya Jam’iyya

Daga: Hamza Musa Yakasai Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Nasir Yusuf Gawuna, ya…