Daga: Hamza Musa Yakasai
Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Nasir Yusuf Gawuna, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a hukumance a yau.
Rahotanni sun ce matakin na zuwa ne a wani sabon salo na sauye-sauyen siyasa da ke gudana a jihar, yayin da ake ci gaba da shirin tunkarar zaɓuɓɓuka masu zuwa.

Sai dai har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, babu cikakken bayani daga bangarorin da abin ya shafa kan dalilan sauyin jam’iyyar.