Hakika babu wata kalma da za ta iya bayyana irin farin ciki da godiyar da ɗalibai, iyaye da al’ummar Kano Ta Arewa suke yi ga Mai Girma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Barau I. Jibrin, bisa gagarumar gudunmawar da yake bayarwa wajen bunƙasa ilimi da inganta rayuwar matasa.
Sanata Barau ya sake nuna cewa shi jagora ne mai hangen nesa da kishin talakawa ta hanyar ɗaukar nauyin ɗalibai zuwa Federal University Dutsin-Ma, inda yake biyan musu kuɗaɗen makaranta tare da tallafa musu da alawus na Naira Dubu Hamsin (₦50,000) a kowane wata domin rage musu wahalhalun rayuwa da mayar da hankalinsu gaba ɗaya kan karatu.
Wannan abin alheri ba kawai tallafin karatu ba ne, wata babbar gudunmawa ce wajen gina makomar matasa, rage zaman banza, yaƙi da talauci da kuma samar da ƙwararrun matasa waɗanda za su zama ginshiƙan ci gaban al’umma a nan gaba. Duk iyayen da ke ganin ‘ya’yansu suna karatu cikin kwanciyar hankali saboda wannan tallafi suna ci gaba da yi wa Sanata Barau addu’a dare da rana.
A yau, dubban matasa suna samun damar cimma burikansu na ilimi ne saboda irin wannan kyakkyawan tsari da Sanata Barau ya samar. Wannan ya tabbatar da cewa jagora nagari shi ne wanda yake amfani da damar da Allah Ya ba shi wajen taimakon jama’a da inganta rayuwarsu.
Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya saka wa DSP Senator Dr. Barau I. Jibrin (Maliya) da mafificin alheri, Ya ƙara masa lafiya, hikima, ɗaukaka da nasara a dukkan al’amuransa. Allah Ya sanya wannan alheri da yake yi ya zamo silar samun rahama da albarka a gare shi da iyalansa.
Barau Maliya, jagoran matasa, ginshiƙin ilimi, abin alfaharin Kano Ta Arewa, kuma gwarzon ci gaban al’umma. Allah Ya ƙara ɗaukaka. Ameen.