DSP Senator Dr. Barau I. Jibrin (Maliya) Ne Ya Samar da Cibiyoyin Karatu na National Open University of Nigeria (NOUN) a Kananan Hukumomi Goma Sha Uku na Kano Ta Arewa.

 

Wannan gagarumin aiki na ilimi ya kawo damar samun karatun jami’a kusa da al’umma, tare da rage wahalar neman guraben karatu da tafiye-tafiye zuwa manyan birane. A shekarar 2021, an kaddamar da cibiyoyin karatun NOUN guda 13 da Sanata Barau ya gina tare da samar musu da kayan aiki a dukkan kananan hukumomin Kano Ta Arewa.

 

Kananan hukumomin da suka amfana sun hada da:

 

Shanono

 

Rimin Gado

 

Tofa

 

Dawakin Tofa

 

Gabasawa

 

Tsanyawa

 

Gwarzo

 

Ghari

 

Dambatta

 

Makoda

 

Kabo

 

Bichi

 

Bagwai

 

Haka kuma, an bayyana cewa cibiyoyin sun samu ma’aikata da motocin aiki domin tabbatar da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, lamarin da ya kara saukaka wa matasa da manya damar ci gaba da karatun digiri da sauran shirye-shiryen ilimi.

 

Godiya da Jinjina

 

Muna mika godiya ta musamman ga Mai Girma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Barau I. Jibrin, bisa wannan gagarumar gudummawa da ya bayar wajen bunkasa ilimi a Kano Ta Arewa. Hakika wannan aiki zai ci gaba da amfanar dubban dalibai na tsawon shekaru masu zuwa, tare da kara habaka ilimi da ci gaban al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Mataimakin Wike Ya Yi Karin Bayani Kan Furucin Da Aka Danganta Da Barazanar Harbin Dan Jarida

Daga: Yakubu Abubakar Gwagwarwa  Mataimakin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) kan Harkokin Hulda…

Sanata Barau: Jagoran Samar da Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma

A tarihin siyasar Najeriya, akwai shugabanni da suke amfani da damar da…

Yanda Baba-Ahmed Ya Yi Watsi da Zargin Neman Tikitin Shugaban Ƙasa

Daga: Abdullahi Bashir Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party…

Shettima: Najeriya da Brazil Na da Ƙaddarar Bai Ɗaya, Dabarun Siyasa Domin Ci Gaba

Daga: Bello Wakili Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jaddada alaƙa ta…