Daga: Zakariyya Adam Jigirya

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya mahukunta da kafatanin ma’aikatan Rediyon Tarayya (Federal Radio Corporation of Nigeria) murnar cika shekaru 75 da kafuwa, yayin da kafar ta cimma wannan gagarumin mataki a ranar 1 ga Afrilu, 2026.

Shugaban ƙasar ya kuma miƙa jinjina ga Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta Ƙasa, tare da daukacin hukumomin da ke aiki kafada da kafada da FRCN, bisa wannan muhimmin biki.

Tinubu ya bayyana FRCN a matsayin wata kafa ko cibiyar watsa labarai mai tasiri, wacce ke taka rawar gani a Najeriya da ma nahiyar Afirka baki ɗaya, inda ya jaddada cewa ita ce mafi girman cibiyar rediyo a Afirka, mai tashoshin FM guda 47 da kuma tashoshi shida na shiyyoyi.

Ya kuma lura da yadda FRCN ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta sadarwar ci gaba tsakanin shugabanni da al’umma sama da shekaru saba’in, takan zama gada mai ƙarfi ta musayar bayanai, ilimi da nishaɗi.

A cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, ya bayyana cewa Shugaba Tinubu na ganin FRCN ta adana tarihin Najeriya ta hanyoyi masu armashi tun daga zamanin mulkin mallaka zuwa bayan samun ‘yanci, inda take zama tushen bincike ga shugabanni, ɗalibai da masana.

Shugaban ƙasar ya kuma yaba da yadda tashar ke zama makaranta ga ƙwararrun masu watsa labarai, furodusoshi da injiniyoyin sauti a nahiyar Afirka.

Yayin da FRCN ke cika shekaru 75, Shugaba Tinubu ya buƙaci cibiyar da ta ci gaba da sauke nauyin da aka ɗora mata, bisa taken ta na, “Uplifting the People and Uniting the Nation.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Soke Kauyawa Day Rusa Walwalar Al’umma ne, Kamata Ya Yi Gwamnatin Kano Da Abba El-Mustapha Su Inganta Ba Rusawa Ba — S. S. Umar

Daga: Sani Magaji Garko Daya daga cikin kwararru a nan Kano Alhaji Salisu…

Dalilan Shugaban Hukumar Alhazai, Farfesa Usman, Na Yin Murabus

Daga: Ibrahim Sani Gama Shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh…

Majalisar Kano Ta Yaba Wa Hukumar Jin Daɗin Alhazai Kan Shirye-Shiryen Hajjin 2026

Daga: MuhammadAdamuAbubakar Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yabawa Hukumar Jin Daɗin Alhazai…

GODIYA DA JINJINA GA DSP SENATOR DR. BARAU I. JIBRIN (MALIYA)

Hakika babu wata kalma da za ta iya bayyana irin farin ciki…