Daga: Yakubu Abubakar Gwagwarwa
Mataimakin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) kan Harkokin Hulda da Jama’a da Kafofin Sadarwa, Lere Olayinka, ya yi karin haske kan wani furuci da Ministan FCT, Nyesom Wike, ya yi yayin wata ganawa da manema labarai a gidan talabijin na Channels Television, inda aka alakanta shi da barazanar harbin fitaccen mai gabatar da shiri, Seun Okinbaloye.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Olayinka ya bayyana cewa Ministan bai taba nufin cewa zai harbi Okinbaloye ba, yana mai cewa furucin da aka ji daga bakinsa ya kasance ne a matsayin karin magana domin nuna fushi kawai, ba tare da wata manufa ta zahiri ba.
Ya kara da cewa Ministan ya riga ya bayyana hakan a fili yayin shirin kai tsaye, tare da jaddada cewa kalamansa sun kasance ne a matsayin karin bayani mai dauke da karin girma (hyperbole) don isar da sako, ba wai barazana ta gaskiya ba.
Olayinka ya ce har ma Ministan da Okinbaloye sun tattauna ta waya bayan shirin, inda dan jaridar ya fahimci ainihin abin da Ministan ke nufi.
A cewarsa, abin da ya bata wa Ministan rai shi ne yadda Okinbaloye, wanda yake girmamawa a matsayin gogaggen dan jarida, ya shiga yanayin magana irin na mai ruwa da tsaki a harkokin siyasa, maimakon ci gaba da gudanar da tambayoyi a matsayinsa na mai gabatar da shiri.
Sanarwar ta kuma nuna cewa dukkanin ‘yan jaridar da suka halarci shirin, ciki har da shugaban ofishin Abuja na gidan talabijin din, sun fahimci cewa furucin bai dauki wata barazana ta hakika ba, har ma suka dauke shi da wasa.
A karshe, Olayinka ya yi kira ga jama’a da su guji amfani da wannan batu wajen yada farfaganda ko bata suna, yana mai cewa duk wani yunkuri na karkatar da ma’anar furucin domin cimma muradun siyasa ba abin karbuwa ba ne.