Daga: Ibrahim Sani Gama
Jam’iyyar APC ta sanar da sake tsara ranar gudanar da zabukan fidda gwani na gwamna a jihohin Bauchi da Kwara zuwa ranar Juma’a, 22 ga Mayu, 2026.

Haka kuma jam’iyyar ta mayar da zabukan fidda gwani na ‘yan takarar Majalisar Dokokin Jihar Zamfara na mazabun Maradun I da Maradun II zuwa ranar Lahadi, 24 ga Mayu, 2026.
A cikin wata sanarwa da APC ta fitar a yammacin ranar Alhamis, jam’iyyar ta ce Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) ne ya amince da sauyin bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki.
Sanarwar ta ce an dauki matakin ne domin tabbatar da gudanar da zabukan fidda gwani cikin gaskiya, tsari, lumana da sahihanci.

Jam’iyyar ta bayyana cewa sauyin ya shafi zabukan fidda gwani na gwamna a Bauchi da Kwara ne kawai, da kuma na ‘yan majalisar jiha a mazabun Maradun I da Maradun II a Zamfara, yayin da sauran zabukan fidda gwani ba su samu wani sauyi ba.