Daga: Abdullahi Bashir
Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Barrista Mohammed Abdullahi Abubakar, SAN, ya fito a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na kujerar gwamna na jam’iyyar APC a jihar domin tunkarar babban zaben shekarar 2027.
Shugaban Kwamitin Gudanar da Zaben Fidda Gwanin Gwamna da na ‘Yan Majalisar Dokokin Jiha na APC a Bauchi, tsohon Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (AIG mai ritaya), John Bassey Abang, ne ya sanar da sakamakon da safiyar Asabar, inda ya bayyana cewa an gudanar da zaben ne a ranar Juma’a, 22 ga Mayu, 2026.
A cewarsa, Mohammed Abdullahi Abubakar ya samu kuri’u 57,517, lamarin da ya ba shi nasara a kan sauran ‘yan takara shida da suka fafata a zaben.
Ya ce tsohon Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, ya samu kuri’u 26,001, yayin da Nura Manu Soro ya samu kuri’u 13,638.
Sauran wadanda suka shiga takarar sun hada da Bala Maijama’a A. Wunti wanda ya samu kuri’u 13,648 da kuma Kabir Baba Ma’aji da ya samu kuri’u 8,157.
Sakamakon zaben ya tabbatar da Mohammed Abdullahi Abubakar a matsayin dan takarar APC na gwamna a Bauchi domin babban zaben shekarar 2027.