Daga: Shehu Suleiman Sharfadi

Gwamnatin Jihar Kano ta jinjinawa al’ummar Ƙaramar Hukumar Kabo bisa yadda suka fito tare da gudanar da sahihin zaɓe a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC da aka gudanar a ranar Asabar a faɗin ƙasar nan.

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Murtala Sule Garo, ne ya bayyana hakan a madadin Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, yayin da ya halarci taron tabbatar da takarar shugaban ƙasa ta Bola Ahmed Tinubu a garin Garo da ke Ƙaramar Hukumar Kabo.

Alhaji Murtala Sule Garo ya halarci wajen zaɓen ne a mazaɓarsa ta Science Day da ke garin Garo domin kaɗa ƙuri’arsa, inda ya bayyana gamsuwarsa kan yadda zaɓen ya gudana cikin tsari da lumana.

Mataimakin Gwamnan ya gode wa al’ummar ƙaramar hukumar bisa amsa kiran da aka yi musu na fitowa kwansu da kwarkwatarsu domin kaɗa ƙuri’unsu ga shugaban ƙasa.

Ya kuma yaba wa al’ummar yankin, inda ya ce jam’iyyar APC ba ta taɓa faɗuwa zaɓe ba a wannan mazaɓa.

Shi ma Baturen Zaɓe na Ƙaramar Hukumar Kabo, Abba Salisu Mai Wake, ya bayyana sakamakon zaɓen, inda ya ce jam’iyyar APC ta samu ƙuri’u 777, lamarin da ya tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓen.

Haka kuma, ya bayyana cewa zaɓen ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana ba tare da wata matsala ba.

Wakilinmu daga Ofishin Mataimakin Gwamnan Jihar Kano ya ruwaito cewa dandazon masu kaɗa ƙuri’a mata da maza ne suka fito domin nuna goyon bayansu ga Bola Ahmed Tinubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Barau Ya Kawo Cibiyoyin NOUN 13 A Kano Ta Arewa, Ya Ƙara Wa Matasa Damar Karatun Jami’a

DSP Senator Dr. Barau I. Jibrin (Maliya) Ne Ya Samar da Cibiyoyin…

Ina Kalubalantar Sanatan Kano Ta Kudu Akan Aikin Titin Kano Zuwa Maiduguri – Hon Bilya Rurum

Daga: Abdulmajid Habib Isah Tukuntawa Guda daga cikin jagororin matasan yankin Rano,…

Cikin watanni 6 Karamar Hukumar Sule-Tankarkar Ta Bunkasa Da Manyan Ayyuka – Hon Tasi’u

Daga: Kabir Getso Shugaban Karamar Hukumar Sule Tankarkar Hon Tasi’u Adamu ya bayyana…

Sanata Barau: Jagoran Samar da Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma

A tarihin siyasar Najeriya, akwai shugabanni da suke amfani da damar da…