Daga: Sani Magaji Garko

Daya daga cikin kwararru a nan Kano Alhaji Salisu Salisu Umar ya ce matakin gwamnatin Jihar Kano da hukumar ta ce fina-finai da Dab’i na soke Kauyawa Day a bukukuwan daurin Aure a jihar Kano kuskure ne, daukar matakin koma baya ne ga cigaban walwalar Al’umma.

Ya ce kamata yayi gwamnatin Jihar Kano ta dauki gabarar tsaftace tsarin don Nishadantar da al’umma maimakon ba rusa shi ba.

S S Umar ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Kano ranar Alhamis.

A cewarsa, hana ko dakatar da Kauyawa Day da Dakatar da wasu shirye-shirye masu dogon zango guda 22 da hukumar ta ce fina-finai ta yi zai Kara saka mutanen cikin takura domin da ire-iren wadannan shirye-shiryen ne mutane suke samun Nishadin kuma ya zama musu masalahar wadansu damuwowi da suke fuskanta.

“Tunda Abba El-Mustapha ya zo hukumar ta ce fina-finai babu wani tsari da ya samar na bunkasa Nishadi ko samar da kudaden shiga ga gwamnatin Jiha, maimakon haka sai ya buge da dakatarwa da Soke hanyoyin walwalar Al’umma, Kai wadannan fina-finan da yake dakatarwa tun yana cikin Yan film ake yinsu, kuma bai taba fitowa ya kalubalanci tsarin ba sai yanzu da ya sami dama ?,” Inji S S Umar.

“Baza ka iya kididdige mutanen da suke da hawan Jini a jihar Kano ba, baza ka iya kididdige masu cutar damuwa ba (Depression) musamman matan Aure ba, ba za ka iya kididdige mutanen da suke fama da shaye-shaye sanadiyyar rashin guraren shakatawa ba, saboda haka duk wadannan matakan da gwamnatin Kano da Abba El-Mustapha suke dauka rusa cigaban al’umma ne, kuma zama su iya kawo matsalar tsaro,” inji Umar.

“Yanzu a jihar Kano babu wani guri da za’a iya kai yara kanana don shakatawa, babu gurin da aka warewa Matasa kawai kamar Yan Shekaru 20, 30, 40 don shakatawa ba, yanzu babu inda aka warewa Mayan Mutane kamar Yan Shekaru 40, 60 zuwa sama don su shakata ba, Dole a samu tarin masu cutar damuwa, gari kamar Kano babu ire-iren wadannan gurare, yakamata gwamnati ta samar aa tsari irin wannan,” inji Umar.

Kwararren ya shawarci gwamnatin Jihar Kano da ta samar da wata ma’aikata dungurungum wacce zata mayar da hankalin wajen cigaba da bunkasa walwalar Al’umma (Ministry of Happiness and social Development).

Ya shawarci gwamnatin Jihar Kano da ta Kago sabbin guraren shakatawa tare da gyara wadanda ake da su domin cigaban walwalar al’umma Jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Gwamnatin Jihar Kano Ta Yabawa Gwamnan Jihar Ogun Bisa Ta’aziyyarsa

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi  Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya…

An bayyana shugabar hukumar taimakekeniyar lafiya ta jihar Kano kachima Dr. Rahila Aliyu Mukhtar amatsyin Mace wadda baza amance da ita ba a harkokin lafiya a jihar Kano.

An bayyana shugabar hukumar taimakekeniyar lafiya ta jihar Kano kachima Dr. Rahila…

Gidauniyar Zuri’ar Sarkin Gini Zakari ya’u ta Kaddamar da bada Tallafin Rance kudi Naira Dubu Hamsin -Hamsin ga Mata 20 Domin Su Zamo Masu Dogaro da Kansu.

An Bayyana Taron Zumunci a Matsayin wata hanya Daka iya kara Dangantaka…

Yanda El-Buhaj Royal Academy Ta Hada Ilimi Da Koyon Sana’o’i, Ta Fara Fidda Dalibai Masu Dogaro Da Kansu

Daga: Kabir Getso ‎Baya ga ingantaccen Ilimi da Dalibi zai samu a Makarantar…