Daga: Kabir Getso

‎Baya ga ingantaccen Ilimi da Dalibi zai samu a Makarantar El-Buhaj Royal Academy akwai tagomashin koyon Sana’ar Hannu Wanda dalibi zai dogara da kansa.

‎Yace Marantar ta samu kyakkyawan tsari na gudanar da koyo da koyarwa da kuma kayayyakin aiki na Zamani, baya ga haka sai mukayi kokarin bullo da wata dabara wacce zata sanya dalibi ya zama mai dogaro da kansa ta fuskar koyon Sana’oi.

‎Yanzu haka Muna da Dalibai da dama wadanda sun kammala makaranta Amma sun dogara da Sana’ar da suka koya Wanda yanzu haka Sun kafu har sun janyo wasu domin koya masu sana’oin.

‎Baya ga koyar da Sana’ar kera Takalmi,akwai Sana’ar kiwaon kaji Wanda ya zanzu gaka muna da katafariyar gona wacce make horar da Dalibai kiwo daban daban.

‎Alh. Abubakar yayi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta rinka saka malaman makarantu masu zaman kansu a wajen horar da Malaman makaranta,domin hakan zai taimaka wajen Samar da ingantaccen ilimi a fadin Jihar Kano

‎Ya kuma godewa iyayan Yara wadanda suke bada cikakkiyar gudunmuwa da hadin kai domin sha’anin Koyo da koyarwa ya inganta a Makarantar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Matsalar Tsaro Na Barazanar Dakile Noman Ridi a Arewacin Najeriya — Danliti Y.Y. Dawanau

Daga: Nura Garba Jibrin Kungiyar ’Yan Kasuwa da Masu Safarar Ridi ta Ƙasa,…

Kungiyar ‘Yan Jarida Ta Kasa Reshen Gidan Rediyon Tarayya Pyramid Za Ta Kulla Alaka Da Kamfanoni Domin Cigaba

Daga: Muhammad Adamu Abubakar  Shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen Gidan Rediyon…

JATA Ta Karyata Jita-Jitar Tsadar Kayayyakin Noma, Ta Ce Ana Sayar Da Su Cikin Rangwame — DG

Daga: Kabir Getso Hukumar Bunƙasa Harkokin Noma Da Samar Da Abinci Na…

‘Yan Bindiga Sun Sace Mamallakin Jaridar Rariya

‘Yan Bindiga Sun Tare Mamallakin Jarida Rariya Sani Ahmad Zangina A Hanyar…