Daga: Nura Garba Jibrin

Kungiyar ’Yan Kasuwa da Masu Safarar Ridi ta Ƙasa, reshen Jihar Kano, ta bayyana cewa, matsalar tsaro na ci gaba da zama babbar barazana ga noman ridi a Arewacin Najeriya.

y

Shugaban kungiyar a kasuwar Dawanau, Ibrahim Muhammad Dawanau, wanda aka fi sani da Danliti Y.Y, ya bayyana haka a hirarsa da wakilinmu.

Ya ce matsalolin tsaro da ke addabar jihohin Borno, Zamfara, Katsina, Sokoto da Yobe na iya jefa harkar noman ridi cikin matsanancin hali har ta kai ga durkushewa.

Ya yi nuni da cewa, baya ga barazanar tsaro, akwai kuma kalubalen rashin kayan aikin noma irin su taraktoci, ingantattun iri da magungunan kashe kwari, abin da ya kara dagula sha’anin manoma.

“Idan aka samar da taki na zamani a farashi mai sauki tare da taraktoci da ingantaccen iri da magungunan kashe kwari, wallahi ni kadai zan iya noma hekta 100, amma a halin yanzu ko hekta 30 ba zan iya nomawa ba,” in ji Danliti Y.Y.

Shugaban ya yi kira ga gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi da su dauki gaggawar matakai domin ceton noman ridi wanda ya ce ke da muhimmanci wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.

A nasa bangaren, mataimakin shugaban kungiyar, Babangida Mansur, ya jinjinawa gwamnatin Jihar Kano musamman kwamishinan kasuwanci bisa irin matakan da suke dauka domin inganta harkokin kasuwanci a kasuwar Dawanau.

Ya bayyana cewa akwai bukatar gwamnatin Kano ta kara mai da hankali wajen horar da ’yan kasuwa kan dabarun karɓar rance daga gwamnatin tarayya da kuma kungiyoyin duniya. A cewarsa, samar da jari ba tare da kudin ruwa ba zai taimaka matuka wajen bunkasa tattalin arzikin jihar, ƙara kudaden shiga da kuma samar da ayyukan yi.

Mansur ya kuma shawarci ’yan kasuwa da su haɗa kai wajen samo hanyoyin da za su inganta harkokinsu, tare da tabbatar da dorewar cigaban tattalin arzikin Arewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Gasar Kofin Tsofaffin ‘Yan Wasan Kwallo Na Kara Zaman Lafiya da Haɗin Kai a Cikin Ƙasa – Inji Hon. Danburan

Daga: Zaharadeen Saleh  Shugaban ƙungiyar shirya gasar tsofaffin ‘yan wasan ƙwallon ƙafa…

Fashewar Tankar Mai A Jihar Neja Wadanda Suka Rasu Sun Karu Zuwa 39 Inda 60 Suka Jikkata – NEMA

Daga: Kabir Getso Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta tabbatar da…

Gwamnatin Jihar Kano Ya Jaddada Aniyarta Wajen Bunkasa Ilimin Fasaha A Fadin Jihar

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo,…

Gwamnatin Jihar Kano Ta Jaddada Aniyarta na Ci Gaba da Samar da Ayyukan Raya Kasa da Inganta Rayuwar Al’umma

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi  Gwamnatin jihar Kano ta jaddada aniyarta na ci…