Daga: Adamu Dabo

 

A yau laraba dubban al’ummar jihar Kano daga sassa daban-daban tareda jerin gwannon kusoshin jam’iyar NNPP suka tarbi Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf a yayin dawowarsa daga aikin Hajjin shekarar 2025

 

Jirgin da ya zo da gwamnan da ayarinsa daga kasar Saudiyya ya fara sauka a jihar ikko da misalin karfe 2:50 na rana.

 

Daga nan sai jirgin ya baro jihar ikko zuwa jihar Kano,inda ya sauka da misalin karfe 3:04 na rana

 

Jim kadan bayan saukar jingin dimbin jama’a da suka tarbeshi suka Kuma raka gwamnan daga filin jirgin sauka da tashi na Malam Aminu Kano zuwa gidan gwamnatin jihar kano a tafiyar kasa da mintuna ashirin zuwa gidan gwamnati ta hanyar titin Murtala Mohammed sai da aka kwashe sama da awa biyar.

 

A yayin tafiyar mai girma gwamna Abba Kabir Yusuf ya dagawa mutane hannu a Wani yanayi na nuni da jin dadi da godiya ga alummar jihar Kano

 

Wakilinmu dake fadar gwamnatin jihar Kano Adamu Dabo ya rawaito cewar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tsaya a shateletalan gidan gwamnatin jihar Kano inda yayi jawabin godiya ga alummar jihar Kano dama magoya bayan jam’iyar NNPP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Gwamnatin Jihar Kano Ta Kaddamar Da Wasan Sada Zumunta Na Shiyyar Arewa Maso Yamma

Daga: Shehu Suleiman sharfadi Hukumar kula da wasanni ta kasa ta shirya…

An Ƙaddamar Da Hukumar Asusun Tsaron Arewa

Daga: Abdullahi Bashir Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewacin Najeriya ta kafa Hukumar Asusun…

Gwamnatin Jihar Kano Ta Yi Haɗin Gwiwa Da Bankin Raya Musulunci Na Duniya Domin Ciyar Da Jihar Gaba

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo,…

Kofarmu a Bude Take Ga Gwamnatoci a Matakai Daban-daban Domin Fassara Litattafan Ilimi Zuwa Harshen Hausa

Daga: Ibrahim Sani Gama Hukumar gudanarwar kwalejin Sa’adatu Rimi dake nan jihar…