Daga: Ibrahim Sani Gama

Hukumar gudanarwar kwalejin Sa’adatu Rimi dake nan jihar Kano ta ta bukaci Gwamnatoci a matakai daban-daban da mayar da hankali wajen ganin fasahar litattafan ilimi zuwa harshen hausa domin daliban arewacin kasar nan su jara fahintar kwasakwasai Yadda ya kamata musamman a arewacin kasar nan.

Shugaban sashen ci gaba da koyan ilimi na kwalejin sa’adatu rimi Dr. Nafiu sani Abas ne ya bukaci hakan a lokacin da yake zantawa da Manema labarai domin tunawa mahukunta amfanun dake cikin fassara litattafan ilimi kamar sauran kasashen duniya.

Dr. Nafiu sani yace idon aka yi duba da sauran kasashen da suka ci gaba kamar kasar China da indiya da makamantansu suna koyar da litattafan ilimi da harshensu na uwa ne domin daliban su fahinci ilimin Yadda yakamata tare da kara daga darajar harshensu a duniya.

Shugaban yace akwai bukatar Gwamnatin tarayya da ta jihar Kano da su tabbatar da sun yi doka a majalisa ta Yadda za”a amince da harshen hausa wajen koyar da dalibai tun daga mataka furaimare da sakandire da Kuma manyan makarantu dake arewacin kasar nan.

Yace akwai kwararrun malamai a jami’u da makarantun kwaleji ilimi na Arewacin kasar da suke da fasahar fassara litattafan ilimi da suka hadar da physics da chemistry da biology da English da dai sauransu.

Dr. Nafiu sani yace a Yanzu haka sun fassara litattafin biology Wanda tuni suka turawa hukumar dake da alhalin amincewa da fassara da buga litattafai ta kasa da ma’aikatar ilimi ta kasa Wanda da zarar sun amince za su fito Shi domin bugawa da rarrabashi a cikin kasuwanni.

Shugaban ya kuma shawarci Gwamnatin tarayya da ta jihar Kano da su baiwa wannan yunkuri cikakkiyar kulawar da ta kamata domin tabbatar da wannan lamari da zai taimakawa dalibanmu na yankunan arewacin kasar nan.

 

Dr. Nafiu sani Abas ya bayyana cewar, Yanzu haka makotanmu na kudancin Najeriya tun daga bangaren yarbawa da Igbo sun Fara wannan yunkuri na ganin sun fassara litattafan ilimi zuwa harshensu na uwa.

Yace yakamata Gwamnaticin mu na Arewacin kasar nan su baiwa wannan tsari mahimmanci, musamman wakilanmu na majalisun tarayya da na jiha da su tallafawa malaman da suke da wannan kwarewa ta fassara litattafan ilimi zuwa harshen hausa domin daliban arewacin kasar nan su Zama suna fahintar kwasakwasai cikin harshensu na uwa.

Daga karshe Shugaban ya bayyana cewar, kofarsu a Bude take a duk lokacin da Gwamnatoci da sauran mahukunta suka nemesu wajen ganin an fassara litattafan ilimi zuwa harshen hausa domin yin gogayya da sauran kasashen Duniya da suka ci gaba, kasancewar yin amfani da harshensu na uwa ya taimaka gaya wajen ci gabansu a duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Dakile Satar Fasaha a Fannin Buga Littattafai

Daga: Ibrahim Sani Gama Gwamnatin Tarayya ta jaddada kudirinta na kawo karshen satar…

Kwamitin Hana Fadan Daba Da Kwacen Waya Sun Gano Wurare 52 Da Ake Aikata Laifuka A Kano

Daga: Ibrahim Sani Gama Janar Gambo Ahmed Mai Addau mai ritaya ya…

2027: Tinubu Zai Lashe Zaɓe Da Gagarumar Tazarar Ƙuri’u Masu Yawa — Ƙaramin Minista

Daga: Abdullahi Bashir Ƙaramin Ministan Raya Shiyyoyi, Uba Maigari, ya bayyana kwarin gwiwarsa…

Remi Tinubu Ta Bukaci Burna Boy, Davido Da Asake Su Kafa Gidauniyoyi Don Taimaka Wa Talakawa

Daga: Sani Idris Maiwaya Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira…