Daga: Sani Idris Maiwaya
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga fitattun mawakan Najeriya da suka haɗa da Burna Boy da Davido da Asake da sauran attajiran masana’antar nishaɗi da su kafa gidauniyoyi domin tallafa wa marasa galihu.

Ta ce duk da cewa mallakar motocin alfarma irin su Maybach da Rolls-Royce abu ne mai kyau, hakan bai kamata ya hana su ware wani ɓangare na arzikinsu don taimaka wa masu sana’o’in dogaro da kai ba.
“Ya kamata mu ga Burna Boy da Asake da Davido da sauran fitattun mawaka suna da gidauniyoyi da ke taimaka wa talakawa. Akwai masu sayar da barkono da kayan lambu da kubewa da gyada da kuma masu soyar da ƙosai da ke buƙatar tallafi,” in ji ta.
Uwargidan Shugaban Ƙasar ta kuma ba da labarin wata matashiya ‘yar jami’a daga Abuja wadda ta fara sana’ar soyar da ƙosai bayan ta rasa aikin yi.

A yayin taron, Sanata Remi Tinubu ta kuma rabawa ƙananan ‘yan kasuwa 2,000 a Jihar Kogi tallafin kuɗi na Naira 50,000 ga kowane mutum domin ƙarfafa sana’o’insu.