Daga: Abdullahi Bashir
Ƙaramin Ministan Raya Shiyyoyi, Uba Maigari, ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa babu wata jam’iyyar adawa ko wata haɗakar siyasa da za ta iya hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu samun nasara a babban zaɓen shekarar 2027.
Maigari ya yi wannan furuci ne a ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da aka gudanar a birnin Jalingo, hedikwatar Jihar Taraba.

Ya ce gwamnatin Shugaba Tinubu na aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su haifar da ci gaba mai ɗorewa a faɗin ƙasar nan, lamarin da, a cewarsa, ya ƙara wa jam’iyyar APC karɓuwa a idon al’umma.
Ministan ya jaddada cewa duk da ƙoƙarin da jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin siyasa ke yi na haɗa kai domin tunkarar zaɓen 2027, hakan ba zai zama barazana ga nasarar Shugaba Tinubu ba.

Ya kuma yi kira ga mambobin APC da su ci gaba da haɗa kai tare da ƙarfafa tushen jam’iyyar a dukkan matakai, yana mai cewa haɗin kai da goyon bayan da jam’iyyar ke samu daga al’umma ne zai tabbatar da sake samun nasara a zaɓe mai zuwa.
Maigari ya ce taron masu ruwa da tsakin APC da aka gudanar a Jalingo ya mayar da hankali ne kan dabarun ƙarfafa jam’iyyar da kuma shirye-shiryen da za su tabbatar da ci gaba da mulkin APC a matakin ƙasa da jihohi.