Daga: Garba Musa Yakasai
Shugaban kungiyar AGSIKA (Kungiyar Taimakon Jam’iyyar APC ta Jihar Kano), Hon. Mus’ab Ibrahim Mai Yadi, ya yi kira ga matasan jihar Kano da su mai da hankali wajen mallakar katin zabe domin tabbatar da damar su wajen zaben shugabanni nagari a jihar da kasa baki daya.

Hon. Mus’ab ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar kungiyar da ke Ummi Plaza, Zoo Road, Kano, inda ya ce kungiyar ta shirya tsaf domin tallafawa matasan da ba su da katin zabe wajen samun shi cikin sauki da tsafta.
“Mallakar katin zabe shi ne hanya ta farko da za ta bai wa matasa damar bayyana ra’ayinsu a zabukan 2027. Kungiyar mu za ta kasance a gaba wajen ganin cewa kowanne matashi da matashiya sun mallaki katin su,” in ji Hon. Mus’ab.
Ya kara da cewa kungiyar AGSIKA za ta hada kai da hukumomi da kungiyoyin matasa domin fara yakin wayar da kai a fadin jihar, musamman a yankunan karkara da unguwanni masu nisa daga birni.

A yayin ganawar, shugaban ya kuma yi kira ga matasa su ci gaba da yi wa jam’iyyar APC addu’a da goyon baya, domin samun nasara a zaben da ke tafe tare da cigaba mai dorewa ga jihar da kasa baki daya.
“APC jam’iyyar ce da ke da shirin ciyar da Najeriya gaba. Ina bukatar matasa maza da mata su tsaya tsayin daka wajen tallata nagarta da akidar jam’iyyar, tare da dagewa da addu’a domin Allah ya ba mu nasara,” in ji shi.

A karshe, Hon. Mus’ab ya tabbatar da cewa AGSIKA za ta ci gaba da kasancewa tare da matasa, musamman wajen tsara shirye-shiryen bunkasa rayuwa da rage zaman banza a tsakanin su.