Daga: Ibrahim Sani Gama
Kungiyar ‘Yan Kasuwar Rimi da ke Jihar Kano ta bayyana cikakken goyon bayan ta ga Gwamnatin Jihar Kano a kokarin da take na tabbatar da tsaro da dakile miyagun laifuka, musamman shaye-shaye da kwacen wayoyin jama’a.
Shugaban kungiyar, Alhaji Saidu Salisu ne ya bayyana hakan a wata zantawa da yayi da wakilinmu a ofishin kungiyar da ke cikin kasuwar Rimi. Ya ce kungiyar ta kuduri aniyar ci gaba da ba da hadin kai ga hukumomin tsaro da Gwamnatin Jiha domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga al’ummar kasuwa da ma baki da ke zuwa domin cinikayya.

Alhaji Saidu ya bayyana cewa kungiyar ta kafa wani kwamiti na musamman da zai rika sa ido tare da tabbatar da tsaron lafiyar jama’a da dukiyoyinsu a cikin kasuwar da kewaye. Ya ce wannan mataki na daga cikin gudunmawar da kungiyar ke bayarwa wajen yaki da aikata laifuka a yankin.
Kazalika, shugaban kungiyar ya bukaci hukumomin tsaro da sauran matakan gwamnati da su tallafa wa kungiyar, ganin irin hadin kai da goyon bayan da take bai wa jami’an tsaro, ciki har da ‘yan sanda na ofishin Shahuci da sauran jami’an tsaro na sa kai.
Ya kara da cewa, “Harkar tsaro ba ta rage ga jami’an tsaro kadai ba, al’umma ma na da rawar da za su taka, saboda matsalolin tsaro sun shafi kowa da kowa.”
Alhaji Saidu Salisu ya kara jaddada cewa kungiyar ba za ta gajiya ba wajen tallafawa kokarin Gwamnatin Jihar Kano na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a ko’ina cikin jihar, domin kuwa babu ci gaba sai da zaman lafiya.

Bugu da kari, shugaban kungiyar ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta kara mayar da hankali wajen tallafawa kananan ‘yan kasuwa da ba su da jarin gudanar da harkokinsu na yau da kullum. Ya bayyana cewa babban kalubale da ke fuskantar mafi yawan ‘yan kasuwa a yau shi ne rashin isasshen jari.
Daga karshe, Alhaji Saidu ya shawarci mambobin kungiyar da su ci gaba da bai wa shugabancin kungiyar cikakken hadin kai domin ciyar da harkokin kasuwanci da walwalar al’umma gaba.
