Daga: Musa Mudi Dawakin Tofa

Malam Ali Yakubu Danjumma ne ya baiyana haka yayin gabatar da nasiha a kan muhimmacin taimakon maraya, wanda kungiyar tsoffin daliban makarantar Firamaren Dawakin Tofa aji na shekara ta alif 1992, da ta gudanar a shekara ta 2025.
Malam Yakubu Danjuma, ya ce akwai misalin hadisi dake baiyana cewa duk wanda ya taimaki maraya zai yi makwabtaka ta kurkusa da Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama, a gidan Aljanna.
Talban Alajawa Alhaji Ibrahim Yaro Dawakin Tofa, ya yi kira ga abokan karatu da su rika bada tallafinsu a duk lokacin da za’a tallafawa rayuwar marayu dama mabukata, saboda hannun karba ya fi hannun bayarwa.

Wakilinmu ya ruwaito cewa an rabawa yara marayu maza da mata tufafin Shaddoji da Atamfofi don sanya musu farin ciki, a sakamakon sun rasa iyayensu maza tun suna marhalar yarinta.